52
Bugu na Ukku | 1438H (2017G) Babban Jagora don Lafiyar masu aikin Hajji da Umrah Ma’aikatar Lafiya

Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

  • Upload
    others

  • View
    2

  • Download
    0

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Bugu na Ukku | 1438H (2017G)

Babban Jagora don Lafiyar masu aikin Hajji da Umrah

Ma’aikatar Lafiya

Page 2: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya
Page 3: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya
Page 4: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Tsarin abubuwan da ke cikiGabatarwa

Matakan lafiya da ya kamata abi kafin gudanar da aikin Hajji da Umrah

Allurran rigakafin da ake yi don aikin Hajji

Riigakafi ga masu aikin Hajji da Umrah a bakin iyakar kasa

Matakan lafiya da ya kamata a dauka lokacin da ake gudanar da aikin Hajji da Umrah

Matakan Lafiya na Musamman don Wasu Marasa Lafiya a lokacin da akegudanar da aikin Hajji da Umrah

Cututtukan da aka fi samu a lokacin da ak yin aikin Hajji da Umrah

Mata da Kananan Yara lokacin aikin Hajji da Umrah

Matsalolin da ke biyo bayan aikin Hajji

Manazarta

1

2

4

6

١0

19

25

40

44

45

Page 5: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya
Page 6: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Jawabin Maigirma Ministan Lafiya Gabatarwa

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Aminci da albarkar Allah su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad.

Allah Madaukaki ya ce a cikin Alkur’ani Maigirma: {…Kuma Hajji a Dakin Ka’aba aiki ne da Allah ke bin bashin dan’adam, ga wadanda ke da halin zuwa (dawainiyar tafiya, abubuwan bukatar rayuwa da wurin kwana) {…[Al-Imran: 97]. Allah Madaukakin Sarki ya girmama wannan kasa mai albarka da Masallatai biyu Masu Tsarki wadanda dukkan mutane daga fadin duniya suke shaukin ziyarta a lokuttan gudanar da ayukkan Hajji da Umrah, wadanda tarukkan dan’Adam ne mafi girma a duniya. Don haka ne gwamnatin da ke da alhakin kulawa da Masallatan Biyu Masu Tsarki a kodayaushe take iya kokarinta da kuma yin amfani da duk abunda take da shi don karbar bakuncin mahajjata da kyau, ta hanyar samar masu duk abubuwan da rayuwa ke bukata da jin dadi don su samu damar gudanar da ibadodin Hajji cikin sauki.

Ma’aikatar Lafiya ta kasar Saudiyya na daya daga cikin hukumomin gwamnati da ke daukar dawainiyar mahajjata ta hanyar kulawa da lafiyar su tun daga saukar su kasar har lokacin komawa kasashen su. Don wannan dalilin, Ma’aikatar ta samar da kusan jami’an lafiya 22,000 ta kuma samar da ma’aikatanta da za su yi ma mahajjata hidima a bangarori daban-daban a tsawon makonnin da ake gudanar da ayukkan Hajji. Kari kan hakan, an samar da wuraren kula da lafiyar mutane da yawa a Makka da Madina da wuraren ibada, da suka hada da assibitoci 25 dake da gadaje 5250 kari kan cibiyoyin lafiya 141 dawwamammi da na wucin gadi. Bayan wannan, an samar da cibiyoyin samar da agajin gaugawa na zamani a Masallaci Mai Tsarki dake Makka.

An samar da kwararrin jami’an lafiya da kayan aikin zamani da ayukkan kula da lafiya kamar sa robar agaji a zuciya, aikin fidar zuciya, hoton binciken lafiyar ciki, da na’urorin wankin koda a dukkan wuraren kula da lafiyar.

Bayan haka, Ma’aikatar ta ba da ra’ayi a wurin daukar matakan kariya da kiyaye lafiyar mahajjata ta hanyar kaddamarwa da daukaka shirye-shirye da yawa na kariya da kara fadakarwa a lokuttan gudanar da ayukkan Hajjin da suka gabata.

Don irin wannan alhaki da muhimmmancin mai da hankali ga daukaka samar da ilimin kula da lafiya a lokacin ayukkan Hajji da Umrah, da sanar da mahajjata abubuwan kula da lafiya da suka dace, da taimaka masu wurin inganta ayukkan su, da muhimmiyar kariya daga kamuwa da cututtuka da annoba, wadanda ke iya takura ma kammala ayukkan ibadar su, Ma’aikatar ta wallafa wata takardar Jagora don bayar da haske a saukake. Jagoran na bayar da haske ne a takaice, kan wasu muhimman abubuwan kulawa ga mahajjata. Muna matukar fatar cewa wannan Jagora zai taimaka ma masu niyyar gudanar da ayukkan Hajji da Umrah da masu ziyarar Madina wurin yin ibadodin su a saukake.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya karbi Hajjin su da Umarar su, Ya kuma gafarta muna baki daya.

Ministan Lafiya

Dr. Tawfiq bin Fawzan Al-Rabiah

Page 7: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

1

Page 8: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

2 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

2

Kafin mahajjata su zo wurin aikin Hajji ko Umrah, ya kamata su kiyaye matakan lafiya daban-daban da bayanai. Ga wasu daga cikin matakan:1. Yin muhimman alluran rigakafi, musamman ga mutanen dake fama da cututtuka da mutane

masu shekaru.

2. Rike isasshen magani, musamman ga marar lafiyar dake bukatar shan magani akai-akai, kamar masu fama da ciwon zuciya da hawan jini, ciwon koda, ciwon asma, ciwon suga da masu fama da matsalar numfashi.

3. Zuwa da isassar sutura. Yawan canja kayan da ke saye ga jikin mutum. An fi son kayan da ba su matse jikin mutum, kuma ba masu kala mai duhu ba.

4. Rike takardar bayanin rashin lafiya da magungunan da likita ya rubuta, wanda zai taimaka ma jami’an lafiya wurin binciken yanayin lafiya idan bukatar haka ta taso.

5. Kula da kayan tsaftace jikinka, kamar tawul, askar aski, sabulu, buroshi da man wanke baki, man shafawa mai yawa, da kuma lema idan bukatar hakan ta taso; an fi son suturar da aka yi da auduga wadda ba ta matse jiki.

6. Kula da maganin kashe kwayoyin cuta, maganin rage zafin jiki, da maganin rage kashe radadin ciwo.

7. Zuwa da na’urar awon ciwon suga.

8. A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya ko sa’a biyu, da kuma motsi da kafafu a lokacin da ake zaune, wanda zai taimaka wurin hana kumburin kafa.

9. Tuntubar likita don tabbatar da cewa ko mutum zai iya yin aikin Hajji.

Ya kamata mahajjaci ya ga likita don tabbatar da ko zai iya gudanar da aikin Hajji.

Matakan lafiya kafin aikin Hajji da Umrah

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 9: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

3Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 3

Wadannan su ne matakan da mahajjaci zai bi a lokacin gudanar da aikin Hajji don tabbatar da lafiyar sa da ta sauran mahajjata:

Muhimman matakan aikin Hajji :

Yin rigakafi da wuri kafin a tafi aikin Hajji na da amfani don kariya daga kamuwa da cututtukan da ke iya yaduwa tsakanin mutane.

A kiyayi zubar da yawu kan dabe.

A kiyayi amfani da na’urorin lantarki masu yawa a wuri daya cikin gidaje.

Idan mutum na fama da tari na fiye da sati biyu, ya kamata a yi masa binciken lafiya kafin ya tafi aikin Hajji, don tabbar da cewa baya dauke da tarin fuka.

A yi amfani da hankici a lokacin da ake atishaya ko tari, musamman a cikin taron jama’a, kamar cikin jirage da motoci, don yin hakan na kare mutum daga kamuwa da cututtukan da ake iya dauka ta hanyar tari ko atishaya.

Page 10: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

4 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

4

Alluran rigakafin da ake yi don tafiya aikin Hajji

Yin rigakafi da wuri kafin tafiya aikin Hajji na da amfani don kare kanka da sauran mahajjata daga kamuwa da cututtukan da ake iya yadawa. Wasu daga cikin alluran rigakafin dole ne a yi su, wasu kuma ana da zabin yin su. Amma duk da haka yana da kyau mutum ya tuntubi likita kafin ya karbi allurar rigakafi.

Kafin tafiya aikin Hajji:1. Mutum ya tabbatar da an yi masa allurar rigakafin ciwon sankarau a kalla kafin

kwanaki 10 na tafiyar sa ko kar a wuce shekaru 3 da yi masa kafin tafiyar sa aikin Hajji. * Tsawon shekarun da ba su kasa shekaru 10 ba idan rigakafin polysaccharide ce, ko shekaru 5 idan rigakafin conjugate ce.

2. Ana ba da shawarar yin rigakafin mura, musamman ga mutanen da ke fama da matsanancin ciwo, da mahajjatanda ba su da cikakkar garkuwar jiki, rashin girman jiki, mata masu juna biyu da yara ‘yan shekaru kasa da 5, da masu fama da shirgegiyar kiba, don amfanin lafiyar su. * A kasar Saudiyya, an wajabta rigakafin mura ga dukkan ma’aikatan lafiya dake harabar da ake gudanar da aikin Hajji a wasu bangarori.

Page 11: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

5Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 5

Allurar Rigakafi

Allurar rigakafin Tetravalent (ACYW) don rigakafin ciwon

sankarau.

Allurar rigakafin ciwon shawara

Allurar rigakafin mura

Rigakafin ciwon shan-inna

Kar ya kasa kwanaki goma

kafin shiga Saudiyya

Kar ya kasa kwanaki goma

kafin shiga Saudiyya

Kar ya kasa mako biyu kafin a shiga

Saudiyya

Sati hudu kafin shiga Saudiyya

Tana bayar da kariyar shekaru

ukku, kuma wajibi ce

Tana bayar da kariya mai tsawo

Za a diga ma mutum maganin rigakafin shan-inna (OPV) ga baki a kan

iyakar kasa bayan an shiga Saudiyya

Dukkan mahajjata da yara masu shekaru biyu zuwa sama, kari kan

mata masu juna biyu

Dukkan mahajjatan da suka fito daga kasashe ko yankunan dake da kasadar yaduwar ciwon shawara,

kamar nahiyar Afirka da ke Sahara, da Amurka

Ana ba da shawarar yin allurar rigakafin mura ga mutanen dake fama da

matsananciyar rashin lafiya da mahajjatan da ba su da cikakkiyar garkuwar jiki,

matan da ke da juna biyu wata 4 zuwa sama da masu fama da ciwon kiba mai tsanani.

Ana yi ma dukkan mahajjatan da suka fito daga wuraren da ake fama da

cutar.

Lokaci BayaniMutanen da za a yi ma

Jerin Rigakafin da ake yi don aikin Hajji

Page 12: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

6 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

6

Rigakafin Hajji da Umrah a Bakin Iyakar Kasa

Hukumar da ta bayarwa: Dokokin Lafiya na Kasa da Kasa

Manufa:Manufar matakan kariyar da ake dauka a bakin iyakar kasa shi ne kiyaye shigowar annobar cututtukan da ke iya yaduwa a tsakanin al’umma cikin Saudiyya baki daya, da kuma wuraren da ake gudanar da ayukkan Hajji da Umrah. Wadannan matakan sun hada da:

Dukkan Matakai:Ya kamata dukkan hukumomin lafiya da ke aiki a bakin iyakar kasa su yi amfani da hanyoyin bincike don tantance kowane bako da shigowar sa. Idan ana zaton wani na dauke da wani ciwo, sai a aika shi zuwa assibiti mafi kusa don duba shi da sanin matakan kariyar da za a dauka. Bayan haka, a bakin iyakar kasa, ana amfani da tsare-tsaren kula da lafiyar al’umma na gaugawa don tunkarar duk wani hatsarin da ke iya yin barazana ga lafiyar al’umma, kuma ana gudanar da tsare-tsaren tare da wasu hukumomin da aka ba horo.

Matakai na Musamman:

(1) Rigakafin ciwon sankarau

Kasashen da ake yi ma: Dukkan kasasheMutanen da ake yi ma: Tsofaffi da yara

Takardar shaidar yin rigakafi: Ana bukatatar baki su gabatar da sahihiyar takardar shaidar yin allurar rigakafin tetravalent ta kariya daga kamuwa da ciwon sankarau, wadda ke nuna cewa an yi allurar ne akalla kwanaki goma kafin a shigo Saudiyya. Rukunan mutanen da ake yi ma:√ Bakin da suka shigo don gudanar da aikin Hajji ko Umrah√ Bakin da suka shigo don gudanar da aikin Hajji da Umrah a yankunan da ake yin ibadodin (Makka, wurare masu tsarki, Madina da Jeddah)

Irin rigakafin da ake yi: Rigakafin tetravalent (ACYW). Wadannan rigakafin dake kasa zabi ne:√ Rigakafi mai suna Polysaccharide, wanda ke bayar da kariya ta tsawon akalla shekaru ukku√ Maganin rigakafi mai suna Conjugate, wanda ke bayar da kariya ta akalla tsawon shekaru biyar.

Page 13: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

7Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 7

A kula: Idan ba a rubuta sunan irin rigakafin da aka yi ba a cikin takardar shaidar yin rigakafi, za a dauka cewa ba rigakafin conjugate ne aka dauka ba, don haka amfanin takardar shaidar na tsawon shekaru 3 ne kawai.

Sauran Matakai: Ana yin rigakafin daukar mataki ne na ciwon sankarau ga wadannan rukunan mutane:1. Ga dukkan mahajjatan da za su yi aikin Hajji da Umrah da suka shigo daga kasashen Afirka da ke da cutar sankarau,

ko an yi masu allurar rigakafin daga kasashen su ko ba a yi masu ba, kasashen su ne: Burkina Faso, Cameroon, Chad, Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya, Côte d’Ivoire, Eritrea, Ethiopia, Gambia, Guinea, Guinea-Bissau, Mali, Nijer, Nijeriya, Senegal, Sudan da Sudan ta Kudu.

2. Wadanda aka yi ma allurar rigakafin sankarau amma ba na tetravalent (ACYW) ba.

3. Mutanen dake da takardar shaidar da aka bayar a cikin lokacin da bai kai shekaru 10 ba, ko fiye da shekaru ukku idan allurar rigakafin polysaccharide ce, ko kuma fiye da shekaru 5 idan allurar conjugate meningococcal ce.

4. Ga mutanen da ba su mallaki takardar da ke tabbatar da an yi rigakafi ba, za a bayar da maganin kariya kamar haka: Tsofaffi: Za a ba su maganin kwayoyin hadiya mai suna Ciprofloxacin 500 mg (wanda za a sha sau daya), kuma ana iya maye gurbin sa da Rifampicin 600 mg, sau biyu ga wuni har na tsawon kwanaki biyu (asha sau hudu), idan akwai wata bukatar yin hakan. Mata masu juna biyu: A yi masu allurar Ceftriaxone 250 mg (a yi masu sau daya) Yara: Za a ba su ruwan maganin Rifampicin kamar haka:

√ Yara ‘yan kasa ga wata 1 : 5 mg/kg a kowace sa’a 12 na tsawon kwanaki biyu (za a yi masu sau 4 ke nan)√ Masu wata daya zuwa sama: 10 mg/kg a kowace sa’a 12 na tsawon kwanaki biyu (za a yi masu sau 4 ke nan)

A kula: Ga dukkan rigakafin da aka ambata a sama, a karanta bayanan da ke cikin takardar da aka gani cikin kwalin allura ko maganin rigakafi cikin natsuwa, kuma a yi aiki da bayanan da ke ciki, musamman wurin ajiyar maganin da yadda za a bayar da shi da kuma irin matsalar da zai iya jawowa.

(2) Ciwon Rawaya

Kasashen da ake yi ma rigakafin: Kasashen Afirka: Angola, Benin, Burkina Faso, Burundi, Cameroon, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chad, Congo, Côte d’Ivoire, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Equatorial Guinea, Ethiopia, Gabon, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Kenya, Liberiya, Mali, Mauritaniya, Nijer, Nijeriya, Senegal, Sierra Leone, Sudan, Jamhuriyar Sudan ta Kudu, Togo da Uganda.

Kasashen nahiyar Amurka: Argentina, Bolivarian Republic of Venezuela, Brazil, Colombia, Ecuador, French Guyana, Guyana, Panama, Paraguay, Peru, Bolivia, Suriname, Trinidad da Tobago

Page 14: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Rukunin mutanen da ake yi ma allurar rigakafin: Tsofaffi da yara

Takardar shaidar yin rigakafi: Kamar yadda dokar lafiya ta kasa da kasa ta tanada, tilas ne dukkan matafiyan da suka fito daga kasashen dake fama da ciwon rawaya su gabatar da takardar shaidar yin rigakafin ciwon rawaya. Tsawon lokacin amfanin takardar shaidar yin rigakafin ciwon rawaya shi ne iya tsawon rayuwar wanda aka yi ma allurar rigakafin, wanda zai fara daga kwanaki 10 bayan yin allurar rigakafin.

Idan ba takardar shaidar yin rigakafin, za a kebe mutum a wuri mai cikakkar kulawa har tsawon lokacin da takardar shaidar za ta fara aiki, ko tsawon kwanakin da ba su wuce 6 ba, daga ranar da mutum ya fito daga yankin da ke fama da ciwon na rawaya. Alhakin ofisoshin kula da lafiya ne su sanar da Babban Jami’in Kula da Al’amurran Lafiya da ke yankin ko hukuma game da dukkan bayanai kan mutunen da abun ya shafa, bayanan za su hada da sunansa, kasar da ya fito, lambar passport dinsa, lambar jirgin da ya shigo, ranar da ya sauka da kuma cikakken bayani game da wurin zaman sa na wucin gadi a Makka ko Madina, da sunan mai masaukinsa.

Sauran Matakai: Jiragen sama, jiragen ruwa da sauran abubuwan zirga-zirga, wadanda ke fitowa daga kasashen da aka sanar da cewa suna fama da ciwon rawaya ana bukatar su gabatar da takardar shaidar cewa suna bin dokar kawar da (sauro) kamar yadda Dokar Lafiya ta Kasa da Kasa (IHR) 2005 ta tanada. Kari kan hakan, Jiragen ruwan da suka fito daga yankunan dake da kasadar yaduwar ciwon rawaya tilas ne su gabatar da takardar shaidar tabbatar da cewa ba su dauke da wani mutum mai ciwon rawaya ko sun kawar da cututtuka a cikinsu, wanda shi ne sharadin bayar da izinin yin zirga-zirga ba wani sanke (wannan ya hada da izinin shiga tashar jirgi da yin lodi ko zirga-zirga da hada-hada).

(3) Ciwon shan’inna

Kasashen Da ya kamata a yi ma:

Afghanistan, Nijeriya, Pakistan, Cameroon, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chad, Guinea, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Al’ummar Laos, Madagascar, Myanmar, Niger, and Ukraine, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Equatorial Guinea, Ethiopia, Iraq, Kenya, Liberia, Sierra Leone, Somalia, South Sudan, Syria da YemenMutanen da ya kamata a yi ma rigakafi: Tsofaffi da yara

• Takardar shaidar yin rigakafi: Dukkan bakin da suka fito daga wadannan kasashe ya kamata su gabatar da shaidar shan maganin rigakafin ciwon shan’inna na polio vaccine (OPV), akalla makonni 4 kafin shiga Saudiyya.

• Irin rigakafin da za a yi masu: Shan maganin rigakafi sau daya na polio vaccine (OPV)

Page 15: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

9Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 9

Sauran Matakai: Ba wani bambancin shekaru da matsayi a wurin daukar rigakafi, dukkan bakin da suka shiga Saudiyya daga wadannan kasashe za su karbi wani maganin rigakafin OPV a bakin iyakar shiga kasar, tare da la’akari da matsalolin da ake iya samu daga shan maganin rigakafin kamar yadda aka tanada cikin takardar dake tare da maganin.

(4) Cutar Zika:

Tun da ya ke ana samun sauron da ke yada cutar Zika a wasu kasashe; musamman na Tsakiya da Amurka ta Kudu, kuma da yake kwayun cutar Zika na yaduwa ta hanyar irin wannan sauron, Dokar Lafiya ta Kasa da kasa ta 2005 ta tanadi cewa dukan Jiragen ruwa da sauran abubuwan zirga-zirga da ke fitowa daga kasashen dake fama da cutar Zika ana bukatar su gabatar da takardar shaidar dake nuna cewa sun kawar da sauro ta hanyar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yarda da ita. Ana sabunta tsarin sunayen irin wadannan kasashen ta hanyar la’akari da yaduwar annoba da bullar cutar Zika a wasu kasashe.

(5) Ciwon zawo da amai:

Kasancewar bullar annobar zawo da amai akasar Yemen, ya kamata a dauki matakan da ke kasa, a iyakokin dake Kudanci. Amfani da hanyoyin bincike don tantance dukkan bakin dake shigowa, musamman a lokuttan gudanar da ayukkan Hajji da Umrah, don gano afkuwar cutar zawo da amai:

1. Amfani da hanyoyin tantance dukkan baki da zarar sun shiga kasar Saudiyya a kowane lokaci, musamman a lokacin Hajji da Umrah don tantance cutar amai da gudawa.

2. Daukar matakan kariya a duk lokacin da ya dace don kebe wadanda ake zaton suna dauke da ciwon, kuma a gaugata sanar da Babban Jami’in Kula da Al’amurran Lafiya, sannan abi dokokin hana yaduwar cuta.

3. Abincin gongoni ko wanda ke kunshe, kuma wanda ke da saukin bincike ne kawai aka yarda a shigo da shi kuma kadan ba da yawa ba, kimanin wanda zai ishi mutum daya kawai a lokacin da ake kan tafiya. Kuma ya kasance da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magungunna ta kasar Saudia (SFDA).

4. Magana da yankunan kasar Saudiyya, Ma’aikatar Ayukkan Gona da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magungunna SFDA don gyara kowane irin ra’ayi dangane da lafiyar muhalli ko lafiyar abinci da ruwa.

5. Daukar samfurin ruwa daga kowane wurin da suke fitowa a bakin iyakar kasa akai-akai don binciken kwayoyin halittar da suke dauke da su. Matakan da ya kamata a dauka a lokacin aikin Hajji da Umrah.

Page 16: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

10 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

10

Matakan Tsafta

A lokacin da mahajjaci ke gudanar da aikin Hajji, ya kan ci karo da al’amurra da mutane da yawa lokacin da ya ke tafiya daga wannan wuri zuwa wancan wurin. Don haka yana da kyau mahajjaci ya kula da lafiyar sa, kuma kar ya taba daukar abubuwa ba kome ba; da yake matsalolin lafiya da yawa na faruwa sanadiyyar nuna halin ko in kula da matakai da bayanai masu saukin bi.

Ga wasu daga cikin muhimman matakan da ya kamata a bi.

Manyan Matakan Tsafta

Muhimman matakan da suka fi dacewa a bi:

• Kula da tsaftar jiki, yawan yin wanka da wanke hannuwa da kyau da ruwa da sabulu ko wasu sinadaran da ake wanke hannu da su don kashe kwayoyin cuta.

• Ka wanke hannunka da kyau, musamman bayan yin wanka, da bayan yin tari da atishaya, da kafin cin abinci da bayan cin abinci da kuma lokacin da ka dawo gida.

• Kar ka zubar da yawu kan dabe, don yin haka hanya ce mai hatsari ta yada kwayoyin cuta, kuma yin hakan bai dace ba.

• Ka yi amfani da hankici a lokacin da kake tari ko atishaya ta hanyar rufe hanci da baki, sannan ka jefa hankicin a cikin shara. Idan ba ka da hankici a hannun ka, ka yi amfani da damtsenka maimakon yin amfani da hannuwanka.

• Ka yi amfani da salga (masai) don yin bayan gari da fitsari, don hana yaduwar cututtukan dake iya yaduwa, rashin yin hakan bai dace ba.

• Ka jefa abubuwan da ba su da amfani da abincin da aka rage cikin shara.• Ka rika canja kayan da ke jikinka a kodayaushe don kauce ma matsalolin lafiya irin su kunar rana. • Ka kiyaye tsaftar gidanka a kowace rana. • Ka tabbatar da kana wanke bakinka da hakoranka a kodayaushe.

Page 17: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

11Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 11

Ka zuba shara a cikin kunshin jikkuna sannan ka jefa su cikin kwandon shara.

Ka yi amfani da abun rufe fuska a lokacin da kake cikin cinkoson jama’a, kuma ka rika canja abun rufe fuskar a kodayaushe kamar yadda kamfanin da ke yin shi ya bayyana, sannan ka wanke hannuwanka da sabulu da ruwa a lokacin da ka cire abun rufe fuska; kuma ka tabbatar da ka cire shi daga bayan kunne ba ta gaban fuska ba.

Ka yi amfani da hankici a lokacin da kake tari ko atishaya ta hanyar rufe hanci da baki, kuma ka jefa shi cikin shara idan ka gama. Idan ba ka da hankici a hannunka, ka yi amafani da damtsen hannunka a maimakon sa hannuwa, don kawar da cututtukan da suka shafi numfashi.

Page 18: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

12 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

12

Matakan Kariya Daga Takurawar Zafi da Bugun Rana Wasu mahajjata na gudanar da ibadodin su kamar irin Dawafi (zagayen Ka’aba) da sa’ayi (tafiya tsakanin Safa da Marwa) da jifar shaidan a cikin turmutsitsi wanda ke kawo tsananin zafi da jawo matsala ga wasu mahajjata, idan aka yi wadannan ibadodin gabanin lokacin cinkoson mutane da lokacin da yanayin zafi bai tsananta ba zai sa mutum ya ji dadin gudanar da ibadarsa, kuma ya kawo zaman lafiya da tsarkakewa. Ya kamata mahajjata su yi isasshen bacci kuma su guji kwantawa a makare wanda ke jawo gajiya da rashin karfin jiki.

Rigakafi:• Rashin shan ruwa na iya sa mahajjata su rasa ruwan jiki mai yawa. Don haka an so su rika shan isasshin

abubuwa masu ruwa (kamar ruwa, matsattsen lemu da sauran su) a kowane lokaci.

• Mahajjata su samu isasshen bacci da hutu, kuma su guji wahalar da kan su da yawa.

• Don kauce ma takurawar zafi da bugun rana, a yi amfani da lema in akwai bukatar hakan. An so a yi amfani da lemomin da kalolin su ba su da duhu. Mahajjaci ya yi kokarin kauce ma shiga cikin rana iya gwargwado.

Don kauce ma takurawar zafi da bugun rana, a yi amfani da lema, a kauce ma shiga cikin rana iya gwargwado. A sha abu mai ruwa da yawa kuma a samu isasshen bacci.

Page 19: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

13Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 13

Rashin Lafiyar da ake samu daga cin Gurbataccen Abinci Wasu mahajjata idan su ka zo yin Hajji ko Umrah sukan kasa bin lafiyayyun hanyoyin sarrafa abincin su, wanda ke haifar da karin yawan cututtukan da ke iya yaduwa, kamar su gudawa, amai, ciwon ciki, majinar hanji da rashin lafiyar da ake samu daga cin gurbataccen abinci.

Rigakafi:• Ka wanke hannuwanka da kyau da sabulu da ruwa kafin sarrafa abinci da kuma kafin cin abinci da bayan

kammala cin abincin, a kuma wanke hannu bayan an kare amfani da bandaki.

• A wanke kayan girkin da aka yi amfani da su.

• A wanke ‘ya’yan itace da ganye da kyau kafin a ci su.

• Kar abar kowane irin abinci a sake, tunda kwari da dabbobi na iya taba shi, kuma yana iya lalacewa.

• A duba lokacin lalacewar abinci da lemon gwangwanin da aka saye.

• A yi amfani da tsaftatatcin ruwa ko ruwan gwangwani wurin sha da dafuwar abinci; ko kuma a tafasa ruwa kafin a yi amfani da su.

• A guji sayen abinci daga masu sayarwa akan hanya, kuma kar a ci abincin da kwari suka taba ko wanda ya lalace.

• A guji aje dafaffen abinci na tsawon lokaci cikin motoci da kuma lokacin da ake zirga-zirga tsakanin wuraren gudanar da ayukkan Hajji. Wannan na daya daga cikin abubuwan dake kawo rashin lafiyar cin gurbataccen abinci a lokacin gudanar da aikin Hajji. A tuna cewa aje dafaffen abinci na tsawon fiye da sa’a biyu cikin daki ko mota na iya haifar da kwayoyin cutar da ke haddasa rashin lafiyar cin gurbataccen abinci. Kamata ya yi a aje dafaffen abinci cikin na’urar sanyaya abinci (firjin) ko kuma adafa abinci dai-dai yawan wanda ake bukata.

• Mahajjata su kula da tsaftar su a lokacin da suke gudanar da aikin Hajji.• Ruwan da za a sha ko dafa abinci da su, su kasance tsaftatatci kuma ba su

dauke da wata kwayar cuta ko gurbacewa.

Page 20: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

14 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

14

Don Kariya daga Rashin Lafiyar cin Gurbataccen Abinci

A guji cin abincin da kwari suka taba ko gurbatacce, kuma a guji sayen abinci daga masu sayarwa a kan

hanya.

Ka wanke hannuwanka da kyau da sabulu da ruwa kafin sarrafa abinci da kafin dafa

shi da bayan cin shi.

A wanke ‘ya’yan itace da ganye da kyau kafin a ci su.

A tuna cewa aje dafaffen abinci na tsawon fiye da sa’a biyu cikin daki ko mota na iya haifar da kwayoyin cutar da ke haddasa rashin lafiyar

cin gurbataccen abinci.

A duba lokacin lalacewar abinci da lemon gwangwanin

da aka saye.

A ci abinci lokacin da aka dafa shi, kuma lokacin da ake bukata, kuma ana iya aje shi a cikin na’urar sanyaya abinci (firjin) a daidaitaccen yanayi.

Page 21: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

15Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 15

Ka tuna da yin amfani da asakenka, kuma kar ka yi amfani da na wasu, wannan ita ce hanya mafi kyau ta kare kai daga kamuwa da cututtukan da ake iya yadawa

masu tsanani.

Wasu mahajjata na amfani da askar da wasu suka yi amfani da ita, wanda kan iya jawo masu daukar cutar ciwon hanta ta (B) da (C). Ka tuna da yin amfani da asaken ka sau daya kawai, kuma ka jefa su cikin kwandon shara da zarar ka gama.

Shawarwari:• Ka zabi wanzamen da ya dace, kuma kar ka taba zuwa wurin wanzaman kan hanya su yi maka aski.

• Ka ce ma wanzame ya wanke hannuwansa da kyau (ta amfani da ruwa da sabulu) kafin yi maka aski ko saisaye.

• Ana bayar da shawarar amfani da askar da ake amfani da ita sau daya kawai. Ka guji dukkan sauran asake, ciki har da wadanda ake canja rezar su bayan kammala kowane askin da aka yi.

• Kar ka hada kayan askin ka da kowa, kamar buroshin cirar gashi, soso, alif, da sauran su.

Matakan Aski da Saisayen Gashi

Page 22: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

16 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

16

Lokacin Hajji cike yake da ayukka da al’amurra. Mahajjata da yawa na taruwa cikin takaitaccen lokaci kuma suna zaman wucin gadi tare a tantunan da ke makwabtaka ko hade da junansu, kuma suna tafiya kusan lokaci daya. Suna zuwa daga kasashe daban-daban, kuma suna magana da harsuna daban-daban, kuma suna da tarbiyyar ilimi daban-daban. Duk wadannan abubuwan da aka ambata na iya haddasa hatsurra da matsalolin lafiya.

Ga wasu daga cikin hatsurran dake yawan afkuwa:

1- GobaraMatakan rage yawan afkuwa ko kariya daga afkuwar gobara:

• A guji hasa wuta cikin tantuna kuma a tabbatar da an yi amfani da wuraren da aka tanada don yin girki. • A jefar da konon sigari a wuraren da aka tanada, kuma a tuna cewa Hajji wata muhimmiyar dama ce ta barin shan

sigari. • Ka nemi sanin hanyoyin da aka tanada don fitar gaugawa a gidan da ka ke, don amfani idan bukatar hakan ta

taso. • A guji adana abubuwan da ke saurin kama wuta ko fashewa a cikin tantuna ko gidaje (kamar tukunyar iskan gas

da sauran su) • A tabbatar da an kashe wutar lantarki a lokacin da za a bar gida, kuma a bar cunkusa na’urorin lantarki a wuri

daya.

2. Hatsurran MotaGa wasu muhimman matakan da ya kamata mahajjaci ko direban mota ya kiyaye:

• A guji gudu kuma a kowane lokaci a kula da mutanen da ke tsakiyar hanya. • A guji hawa saman rufin motoci da abubuwan hawa, musamman a lokacin da za a bar Arafat da Muzdalifah. • Idan ana tafiya ne a kasa, mahajjaci ya yi nesa da hanyar da aka tanada don amfanin motoci da abubuwan hawa.

Matakan Tsaro

Page 23: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

17Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 17

Mahajjaci ya yi iya kokarinsa na kauce ma tafiya cikin cinkoson jama’a, don yin haka na rikitarwa da jefa sauran mahajjata cikin hatsari.

3- Gurjewa da karaya

• Kar mahajjaci ya tsaya saman tsaunuka da wurare masu tsawo, ya kuma guji hawan manyan duwatsu, don yin hakan na iya jefa rayuwarsa cikin hatsari.

• A guji ture-ture da ingizar juna a lokacin da ake sauri, don yin hakan shi ne babban abunda ke haddasa samun gurjewa da karaya.

• A zabi lokacin da ya dace na yin tafiya da yin ibadodi, kuma a yi amfani da abunda Musulunci ya yarda da shi idan aka cika ka’idojin shi.

• A guji bacci akan hanyoyi da gefen titin mota, ko bacci karkashin motoci don tsaron lafiyar mahajjata. • Ka daga lemarka sama a lokacin da kake cikin jama’a don kar ka raunata wasu mutane. • Ka kasance mai tausaya ma mutanen dake da rauni, kamar marar lafiya, tsofaffi, mata da yara kanana.

Page 24: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

18 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

18

Adana magani yadda ya dace:Kamata ya yi mahajjaci ya kula da yadda zai adana maganin da yake sha kodayaushe ko na wucin gadi, musamman ma cikin yanayin zafi. Ana sayar da kananan jikkunan ajiyar magani a kasuwa.

Iftirash (muguwar kwanciya):Iftirash (muguwar kwanciya) daya ne daga cikin halayen dake da lahani wadanda ake gani a lokacin gudanar da aikin Hajji. Wasu mahajjata na kwantawa su yi bacci a kan hanyoyi, karkashin gadoji da kan abubuwan hawa a duk tsawon lokacin aikin Hajji. Wannan na taimaka ma yaduwar annoba da cututtukan da ake yadawa. Mahajjatan dake da wannan al’adar na iya samun matsalar takurawar zafi da bugun rana, kuma hakan na haddasa wahalar wucewar abubuwan hawa, motocin daukar marar lafiya da motocin jami’an tsaro. Wannan na taimakawa wurin yaduwar annoba da cututtukan da ake iya dauka daga wani.

Barin Shan taba:Ka tuna lokacin Hajji wata muhimmiyar dama ce ta barin shan taba da za ka iya cin ribarta. Lahanonin shantaba hujjoji ne ga kowa. Lokacin Hajji shan taba na zama hatsari mai yawa ga mai sha da kuma mutanen da ke zagaye da shi, saboda cunkoso da kusancin gidajen mahajjata.

Ko sa Marufin Fuska na da amfani ga mahajjata? A sa Marufin fuska da kyau. A rika canja su akai-akai (Bayan kowace sa’a shidda) ko idan sun yi datti, kamar yadda kamfanin dake yin su ya bayyana, tare da wanke hannuwa da ruwa da sabulu bayan an cire su. A cire su ta bayan kunnuwa ba ta gaba ba.

Ana ba masu fama da ciwon sanyi shawarar amfani da marufin fuska don taimakawa wurin hana yaduwar cututtuka.

Page 25: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

19Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 19

Matakan Lafiya na Musamman don Wasu Marar Lafiya a lokacin Hajji da Umrah.Wasu marasa lafiya na bukatar kulawa ta musamman a lokacin gudanar da ayukkan Hajji da Umrah .

Matakan Lafiya don Masu Fama da Ciwon Zuciya:Gaba daya, wanda ke fama da ciwon zuciya wanda bai yi muni ba na iya gudanar da ibadodin Hajji. Amma duk da haka ana ba shi shawarar bin wadannan matakan da ke biye:

• Ya ga likita don tabbatar da cewa ko zai iya gudanar da aikin Hajji.

• A kodayaushe ya kasance kana tare da isasshen maganinka, ka adana su yadda ya kamata a wurin da ba za ka manta ba.

• Ka kasance tare da takardar cikakken bayanin yanayin lafiyar ka da irin maganin da kake sha.

• Ka guji yin duk wani aikin wahala, kuma ka yi amfani da keken guragu a lokacin da kake yin Dawafi (zagayen Ka’aba) da Sa’ayi idan ka gaji, kamar yadda Musulunci ya tanada.

• Ka rage sa abu ga rai da kuma garaje, kuma ka tuna cewa ‘yanci na daya daga cikin alamomin mahajjaci.

• Ka ci abincin da ba shi da maiko da gishiri, kuma ka kiyaye abincin da likitan ka ya ba ka shawarar ci.

• Ana ba da shawarar cewa ka zo da daya daga cikin ‘yanuwanka ko abokai a lokacin da kake gudanar da ibadodi ko da bukatar gaugawa na tasowa.

Idan ka ji wani ciwon kirji ko wahalar numfashi, ka samu hutawa. Idan ciwon kirjin ya yi muni, ka gaggauta zuwa asaibiti.

Page 26: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

20 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

20

Masu ciwon suga na iya aikin Hajji ko Umrah idan an binciki yanayin lafiyarsu kuma aka tabbatar da cewa za su iya yin ibadodin. Amma duk da haka, su kula da wadannan abubuwa:

• Saukar sugan jiki sanadiyyar wahala, shiga cikin rana da canjin abincin da ake ci.

• Raunukan wahala ko gyambon kafafu da sauransu, sanadiyyar yawan tafiya da cinkoson mutane.

• Kunar rana wanda ke da saukin samun masu ciwon suga sanadiyyar cinkoson mutane, yawan gummi da canjawar yanayin suga a cikin jiki.

Ga wasu matakai don masu ciwon suga su kauce ma wadancan matsalolin: • Ka sa munduwa a hannu ko ka rika katin da zai nuna cewa kana da ciwon suga da maganin da kake sha

don nema maka taimakon da ya dace idan bukatar hakan ta taso.

• Ka zo da na’urar awon sugan jiki don tantance yawan sugan jiki a kowace rana kuma akai-akai, musamman idan kana jin yanayin suga ya canja.

• Ka rike cikakken bayanin yanayin lafiyar ka, kuma ka fada ma mutanen da ku ke zaune gida daya da su, da likitan tawagar ku cewa kana da ciwon suga.

• Ka sha isasshen maganin suga kuma ka ci irin abincin da likitan suga ya ba ka shawarar ci.

• Ka tabbatar da ka adana sinadarin insulin a wuri mai sanyi kamar cikin sundukin adana kankara (thermos), ko ka sa cikin akwatin sanyaya abinci (firjin) a gidan da ka ke.

• A lokacin aikin Hajji, ka sa safar kafa don kare kafafunka daga samun rauni, kuma ka guji tafiya ba takalmi.

• Ana shawartar ka cewa kar ka fara Dawaf (zagayen dakin Ka’aba) ko Sa’ayi (tafiya tsakanin Safa da Marwa) idan ba ka sha magani ba ko cin isasshen abinci, don kauce ma ragewar suga a cikin jiki.

Matakan Lafiya don Mai ciwon Suga:

Page 27: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

21Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 21

• Ka cigaba da cin muhimmin abinci marar nauyi kamar yadda likita ya tsara maka ka ci, a lokacin tafiya da lokacin aikin Hajji don kauce ma ragewar sugan jiki maitsanani.

• Ka tsayar da ibadodin da ka ke yi na wucin gadi idan ka fara jin alamun ragewar sugan jiki, kamar yin rawar jiki, jin kamar za ka fadi, da ciwon jiki da kasala, jin yunwa kwatsam, yawan gumi da gani buji-buji, kuma ka dauki matakin magani da zarar ka ji hakan.

• Ka cigaba da shan ruwa da yawa kamar yadda ya dace.

• Ka zo da maganin kashe kwayoyin cuta don magance raunukan fatar jiki idan sun afku, idan gyambo ne sai ka tuntubi likitan ciwon suga.

• Ka yi amfani da na’urar askinka ta lantarki maimakon reza don kauce ma samun raunuka da kamuwa da cuta gwargwadon yadda za ka iya.

Menene maganin ciwon karancin sugan jiki? Idan hankalinka bai gushe ba, kana iya yin wadannan abubuwan:

• Shan kofin matsattsen lemu mai zaki, ko inabi, ko abarba ko kuma hade-haden ‘ya’yan itace.

• Ka na iya shan cokali biyu na zuma,

• Ko ka sha cokali biyu na suga, ka zuba cikin kofin ruwa ka motse, ko

• Ka sha kwayu 2 zuwa 5 na sinadarin glucose (ka na iya sayen su a shagon sayar da magani).

Idan hankalin mai ciwon suga ya gushe, a gaggauta kai shi assibiti ma fi kusa.

Page 28: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

22 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

22

A lokacin aikin Hajji ko Umrah, mai ciwon asma yakan fuskanci yawan matsalar yin numfashi da kyar, wannan ya na faruwa ne saboda dalilai da dama kamar: kasancewa cikin wurin cinkoson mutane mai kura da gurbataccen hayaki dake fitowa daga abubuwan hawa, yin tafiya mai tsawo da ciwon hakarkari wanda ke iya karuwa saboda taron jama’a.

Ana shawartar masu ciwon Asma su yi wadannan abubuwan:• Ka sa munduwar hannu mai dauke da sunanka da shekaru, da rashin lafiyar ka da kuma maganin da kake

sha.

• Ka ga likitan matsalar numfashi don tabbatar da daidaituwar yanayin lafiyarka da kuma sanin ko za ka iya yin tafiya da irin matakan da ya kamata ka dauka idan asma ta taso maka.

• Ka tafi da magani isasshe, musamman ma maganin bututun da ake shakawa.

• Kafin yin kowane irin aiki ana ba ka shawarar yin amafani da maganin kyautata numfashi, musamman ma a lokacin yin Dawafi (zagayen Ka’aba) da jifar shaidan.

• Ka rika tsayawa ka na hutawa.

• Ka guji shiga cikin cinkoson mutane don kauce ma tasowar ciwon asma.

• Ka gaggauta yin amfani da maganin bututun shakawa da zarar ka ji alamun tasowar ciwon asma kuma ka nufi assibiti mafi kusa idan ka fuskanci samun ciwon asma mai karfi.

Idan mai ciwon asma ya ji alamomin tasowar ciwon, ya hanzarta yin amfani da maganin bututun shakawa kuma ya nufi assibiti mafi kusa idan ya fuskanci tasowar

ciwon asma mai tsanani.

Matakan da ya kamata Masu Ciwon Asma (daukewar numfashi) su dauka

Page 29: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

23Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 23

Sau da yawa, alamomin ciwon kin jinin wani abu na iya karuwa sanadiyyar kasancewar wasu abubuwa a wurin da mutum yake, kamar hayaki, kura, abinci, sinadaran kimiyya da sauran su, kuma su na shafuwar fatar jiki, idanu, hanci da kirji (asma). A lokacin aikin Hajji da Umrah wadannan alamomin na iya karuwa saboda cinkoson mutane, kura da datti, yanayi, hayakin motoci da sauran su.

Matakan da za a bi don rage irin wadannan matsalolin: • A guji wurare da lokuttan da ke haddasa kin jini, kamar shiga cikin rana da cinkoson mutane.

• Game da matsalar kin jinin wani abu na fatar jiki ko hanci da idanu: Marar lafiya ya zo da maganin da ya dace (kwayoyi, maganin fesawa ga hanci, ko maganin digawa ga ido) kamar yadda likita ya tsara. Ciwon kin jini ba wata babbar barazana ba ce ga mahajjaci sai dai idan ciwon asma ne ya taso masa.

• Matsalar kin jinin abinci: Idan matsalar kin jinin wani abinci ne, maganin da ya dace shi ne barin cin irin wannan abincin.

Mai fama da ciwon kin jinin wani abu ya guji shiga wurare da lokutta, da ayukka ko cin abincin da jininsa ba ya so, ko shiga cikin rana da cinkoson mutane.

Matakan da ya kamata masu ciwon kin jinin wani abu su dauka:

Page 30: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

24 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

24

Shawara ga masu fama da ciwon rashin fitar fitsari, da kasawar koda da duwatsun koda:• Ka tuntubi likitan mafitsara don tabbatar da cewa ko za ka iya yin aikin Hajji kuma ya baka matakan lafiya

da ya kamata ka bi.

• Ka zo da magungunan da aka rubuta maka, kuma ka adana su a wuri mai kyau wanda ba za ka manta ba.

• Ka tsare shan magungunan cikin lokaci a kodayaushe.

• Ka sha abu mai ruwa da gishiri dai-dai da yadda likita ya kayyyade maka.

• A guji shiga rana haje-haje na tsawon lokaci don kauce ma karewar ruwan jiki da gishiri.

• A guji cin nama da yawa don kar ya shafi aikin koda.

• Ka tuntubi likitan tawagarku ko cibiyar lafiya ko assibiti mafi kusa idan wata matsala ta taso kamar matsalar ciki da ta mafitsara.

• Ka nufi cibiyar lafiya ko assibiti mafi kusa idan bukatar hakan ta taso.

Masu fama da ciwon kasawar koda:

Aikin Hajji ko Umrah zai yi matukar wuya gare ka, zai iya zama barazana gare ka, sai dai in likitan tawagarku ya na bin ka, kuma tun farko ka shirya da wata assibiti da za ta yi maka wankin koda.

Masu fama da ciwon duwatsun koda:

Ana son mutum ya sha abu mai ruwa da yawa ya kuma kauce ma shiga cikin rana. Kuma ka rika yin wasu ibadodin da marece a lokacin da rana ta fadi, ko ka sa wani ya yi maka kamar yadda Musulunci ya tanada.

Ka sha abu mai ruwa da gishiri yadda likitan mafitsara ya shawarta, ka guji shiga rana gwargwadon hali, don taimaka ma lafiyar jikinka kula da ruwa da gishirin da ke

cikinsa.

Matakan da ya kamata Mai Ciwon Koda ya dauka

Page 31: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

25Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 25

A lokacin da ake gudanar da ibadodin Hajji da Umrah mahajjata na da kasadar kamuwa da wasu cututtukan dake da alaka da yanayin lokacin Hajji, wadanda suka hada da mura, sanyi, rashin lafiyar cin gurbataccen abinci, kunar rana, bugun rana, kudar zafi, saukar sugan da ke cikin jini, ciwon makoshi da gudawa.

Cututtukan Numfashi:Wadannan cututtukan sune aka fi samu a lokacin gudanar da aikinHajji. Su na yaduwa ne ta hanyar tari da atishaya da mutane ke yi. Sun kasu gida biyu kamar haka:

1. Cutar numfashin sama, kamar irin ciwon sanyin da aka saba yi, kumburin hanyoyin iskan cikin huhu da shakewar murya: Wadannan ba su haddasa wasu matsaloli, amma suna yi ma mahajjata lahani, kuma suna jawo kasala.

2. Matsalar kumburin hanyoyin kasa na numfashi (kamar ciwon hakarkari): Ba a cika samun wadannan cututtukan ba amma sun fi tsanani. Alamominsu su ne: Tari da majina, zazzabi ko wahalar numfashi. Idan ba a magance su ba, wadannan alamun za su jawo matsaloli masu tsanani.

Cututtukan da aka fi samu a lokacin aikin Hajji da Umrah:

Page 32: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

26 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

26

Rigakafin cututtukan numfashi:• A guji zama da masu ciwon numfashi kuma a guji yin amfani da kayan da suke aiki da su.

• Ka guji taba idanunka ko hanci da hannuwanka har sai ka wanke su da kyau.

• Ka guji shiga cikin cinkoson mutane.

• Kar ka sha ruwan kankara.

• Ka guji fuskantar iska kai tsaye, kamar irin na na’urar sanyaya daki, musamman ma idan ka yi gumi. Babban canji a cikin yanayin jiki na kawo illa ga lafiya.

Idan aka samu daya daga cikin wadannan cututtukan (kamar sanyi da mura), sai abi wadannan matakan dake biye: • A sha ruwa da yawa da abu mai ruwa-ruwa wanda ke da zafi, kuma a guji shan abu mai tsananin sanyi.

• A samu yin isasshen bacci.

• A sha maganin rage zafin jiki da radadin ciwo (sai dai idan har likita ya rubuta wani magani) kamar yadda likita ya ba da umurni.

• A magance matsalar toshewar hanci a cikin takaitaccen lokaci, saidai in wata matsala ta hana hakan, kamar hawan jini ko matsalar karancin jini.

• A sha maganin tari idan akwai bukatar hakan, musaman ma ga busasshen tari (wanda ba majina) ko idan yana da tsanani lokacin da ake bacci.

• A guji shan maganin kashe kwayoyin cuta sai in likita ne ya ce a sha.

• A tuntubi likita da an fara ganin alamomi masu tsanani.

Cututtukan numfashi su ne wadanda aka fi samu a lokacin da ake yin aikinHajji. Ba a cika samun ciwon kumburin hanyoyin numfashi na kasa (kamar ciwon harkarkari) ba, amma sun fi tsanani.

Cututtukan hanyoyin numfashi na sama sun hada da ciwon sanyin da anka sabayi, kumburin hanyoyin iska da shakewar murya.

Page 33: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

27Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 27

Cutar Numfashin da ake samu a kasahen Gabas ta Tsakiya

Alamomin Cutar Numfashin da ake samu a kasahen Gabas ta Tsakiya:• Zazzabi da tari • Gudawa• Karanchin numfashi • Toshewar hanci da makoshi

Yadda ya ke yaduwa:Kamar ciwon mura, kwayar wannan cutar na yaduwa ne ta hanyar mu’amala kai tsaye da mutanen da ke fama da rashin lafiyar, danshin tari ko atishayar da aka yi. Wata hanyar kamuwa da cutar ita ce taba wurare da abubuwan da cutar ta gurbata da hannu sannan a taba baki ko hanci ko idanu. Haka kuma, rakumma na daya daga cikin abubuwan dake yada cutar.

Hanyoyin Rigakafi:1. Ka wanke hannuwanka da kyau da ruwa da sabulu, ko da sinadarin kashe kwayoyin cuta, musamman bayan an yi

tari ko atishaya ko bayan an fito daga bandaki. Kuma ka wanke hannuwanka kafin ko bayan ka rika ko sarrafa abinci.

2. Ka yi iya kokarinka na kauce ma taba idanu ko hanci ko baki da hannunka.

3. A tabbatar da an dafa naman rakumi da kyau, kuma an tafasa madarar su kafin a sha.

4. Ka yi amfani da hankici a lokacin da kake tari ko atishaya don rufe baki da hancinka, kuma ka jefar da hankicin cikin kwandon shara tare da wanke hannuwanka bayan ka kare. Idan kuma ba ka da hankici, an so ka yi tari ko atishaya a kan damtsen ka ba a cikin tafin hannu ba kuma bakinka ya kasance a rufe.

5. Za ka yi amfani da marufin fuska idan ba ka da lafiya ko za ka ziyarci marar lafiya ko za ka yi amfani da kayan aikin marar lafiya kawai.

6. Ka tsare yin tsafta.

7. A wanke ‘ya’yan itace da ganye da kyau da ruwa kafin a ci su.

8. Ka kula da sauran dabi’un lafiya kamar cin abinci mai gina jiki da motsa jiki, da samun isasshen bacci, saboda hakan na kara taimaka ma garkuwar jiki.

Page 34: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Muhimman Matakan Lafiya na yin amfani da Marufin Fuska

Wane lokaci ne za ka yi amfani da marufin fuska?• Lokacin ziyarar marar lafiya

• Lokacin da ka kamu da wata cuta

• Wurin taron al’umma

Yadda ya kamata a yi amfani da marufin fuska• Ka wanke hannuwanka da kyau kafin ka sa shi.

• Ka zabi wanda ya yi dai-dai da fuskarka, kuma an bayar da shawarar yin amfani da mai dan karfe wurin kwantawar hanci.

• Ka rike shi da hannu daya kuma ka a za shi yadda zai rufe hanci, gemu da baki.

• Ka ja kyallen roba da ke kasa, ka aje shi karkashin hancinka, sannan ka ja kyallen robar sama ka laka shi saman kai daga baya ta hanyar yin amfani da dayan hannunka.

• Ka danna dan karfen da ke makale a hankali har ya zauna kan gorar kashin hancinka, shike nan marufin fuska ya zauna daram a fuskarka.

• Ka jarraba marufin fuskarka ta hanyar a za hannunka a kan iyakokin marufin fuskar sannan ka ja numfashi don tabbatarwa ko iskan da kake shaka na fitowa ne daga gefen fuska.

• Ka cire marufin fuskar ta bayan kunnuwa maimakon cire shi ta gaban fuska.

• Ka rika canja marufin fuska bayan tsawon kowacce sa’a shidda, ko idan ya yi datti.

• Ka tabbata cewa ka wanke hannuwanka da ruwa da sabulu bayan ka cire marufin fuska.

Page 35: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

29Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 29

Cututtukan matsalar narkewar abinci (Gudawa, Gobarar ciki, Tashin zuciya da Amai)Wadannan cututtukan na faruwa ne sanadiyyar wasu kwayoyin cutar da ke yaduwa ta hanyar gurbataccen abinci da abun sha. Wadannan cututtukan sun hada da ciwon gudawa da amai.

Rigakafi:• Ka tabbatar da tsafta da lafiyar abincinka.

• Ka kiyaye tsaftar jikinka, ka wanke hannuwanka da kyau, kuma ka guji yin amfani da kayan aikin wasu.

• Ka guji shan madarar da ba a tafasa ba, da abincin da kalar sa ko dandanon sa ya suka canja. Ka guji cin abinci mai maiko da suga, kuma ka tabbar da ka dafa nama da kyau.

• Ka ci sabbin ‘ya’yan itace da ganye.

• Ka sha abu mai ruwa da yawa, kamar ruwan sha da matsattsen lemu.

Magance Gudawa:Ka sha abu mai ruwa da yawa don kauce ma karewar ruwan jiki. Ka nufi cibiyar lafiya ko assibiti mafi kusa idan gudawa ta yi tsanani da alamun karewar ruwan jiki, don samun karin ruwa da sinadarin karin ruwan jiki.

Ka kare kanka daga kamuwa da cutar gudawa, tashin zuciya da amai da sauran su, ta hanyar cin lafiyayyen abinci, tsare tsaftar jiki, kamar wanke hannuwa da kauce

ma amfani da kayan aikin wasu.

Page 36: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

30 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

30

Ciwon zawo da amai (cholera)

Alamomi:• Alamomin cutar gudawa da amai na faruwa ne nan take da gudawa mai kamar ruwa, wani lokaci ana ce

mashi bahayar ruwan shinkafa (ba tare da wata alama a ciki ba), sannan amai ya biyo baya.

• Tsananin gudawa da amai zai sa jiki ya rasa ruwa da gishiri (karewar ruwan jiki) daga nan sai a rasa rayuwa idan ba a maye gurbin ruwan jikin da suka zube ba.

• Wani ciwon gudawa da amai ya kan zo da sauki ba tare da haifar da wasu matsaloli ba ga yara.

Rigakafi:• Ka tsare dabi’un lafiya da suka shafi abinci da abun shan ka, da wurin zamanka da kula da tsaftar jikinka.

Ka wanke hannuwanka da kyau da sabulu da ruwa kafin ka ci da bayan ka ci abinci don hana yaduwar cuta.

• Kodayaushe ka wanke hannuwanka da kyau da ruwa da sabulu bayan ka gama bahaya.

• Ka yi amfani da tagardar goge-goge (ko takardar tsaftar kici) don rage dattin yatsu. Idan babu wurin yin bahaya, a bizne bahayar da aka yi a kasa bayan an gama, kuma ya kasance nesa da wurin da ake samun ruwan sha.

• Ka kula da cikakkar tsafta a wurin sarrafawa da hada abincinka, kuma ka sanyaya shi da kyau. Haka kuma, ka tabbatar da ka adana ganye da ‘ya’ayan itace da kyau wadanda za a ci da sanyi. Wannan matakin na amfani ne ga dukkan gidaje da wuraren cin abincin al’umma. Idan ba ka tabbatar cewa ko ma’aikata na bin matakan lafiya ba, ka zabi dafaffen abinci ka ci shi da zafi.

• Ka wanke ganye da kyau kuma ka kankare bayan ‘ya’yan itace kafin ka ci su.

• Ka kula da lafiyar abinci da abunsha ta hanyar rufe su don hana kuda sa kwayoyin cuta a kan su.

• Ka kawar da kuda tare da wuraren da suke hayayyafa, ta hanyar kwashe shara da zuba ta a cikin kwandon shara.

• Ka yi amfani da tsaftatatcin ruwa ko ruwan gongoni don sha da dafa abinci, ko kuma a tafasa ruwa kafin ka yi amfani da su.

Page 37: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

31Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 31

Maganin Rigakafi:Akwai maganin rigakafin da ake sha guda biyu kuma suna bayar da kariya ta watanni da yawa.

Muhimmancin Sanarwa:1. Gane hanyoyin yaduwar cututtuka (kamar hanyar samun ruwan sha ko abinci), da kuma daukar matakan

da suka dace wadanda za su iya hana karin yaduwar cuta daga ita wannan hanyar.

2. Gane mutanen da suka kamu da cuta don kare yaduwar cuta dagare su.

3. Gane mutanen dake hulda da mutanen da suka kamu da cuta da daukar matakan rigakafi don kawar da yaduwar cutar.

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 38: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

32 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

32

Cutar Fatar JikiCinkoson mutane, yanayin zafi, yawan gumi, raba, da yawan shiga rana a lokacin aikin Hajji na kara yawan kamuwa da cututtuka a tsakanin mutanen da suka zo daga sassa daban-daban na duniya, musamman ma cututtukan fatar jiki.

Wadannan sune cututtukan fatar jiki da aka fi samu a lokacin aikin Hajji:

1- Bula (Gurjewa a gabobin jiki):

Wannan matsalar fatar jiki ce da aka fi samu a tsakanin mutane masu manyan jiki ko kiba ko masu ciwon suga, a karkashin hamuta da nono (musamman ga mata), ga cinyoyi da wasu wuraren dake da saukin kamuwa da cuta na jikin maza. Ga wadannan cututtukan, fatar jiki za ta kumbura ta yi ja, kuma idan cutar ta yi kamari, alamomi masu zafi kwarai za su fara bayyana, kamar fitar ruwa, sai radadi ya biyo baya.

Rigakafi da Magani:• A bar iska ya rika zagaya cinyoyi da karkashin hamutta

• Kula da tsaftar jiki

• Shafa man da ya dace a wadannan wurare kafin a yi tafiya.

• Fesa man hana kumburar fata bayan mazauni.

Idan ka samu irin wannan cutar za ka iya shafa man da aka yi don irin wannan matsalar, kuma ka wanke wurin da abun ya shafa da ruwa da sabulu kafin ka shafa magani, ka cigaba da yin hakan.

2- Kunar Rana:

Mahajjaci na samun kunar rana ne idan ya shiga cikin rana kai tsaye na tsawon lokaci, yana haddasa kumburar fata da mayar da fata ja. Ana ganin wannan a wasu sassan jikin mahajjata da suka bari zafin rana ya doke su. Amma kuma, kunar rana na yin bodalla, ya ja ruwa wanda ke da zafi sosai. Cutar tafi yawa a tsakanin mutane farar fata da bakin da suka fito daga kasashen da ba su da zafi.

Ka kiyaye fatar jikinka daga kumbura da kunar rana a lokacin aikin Hajji ta hanyar barin iska zagayawa a kafofin jikinka.

Page 39: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

33Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 33

Rigakafin kunar rana a jiki:• Ka yi amfani da lemar ka akai-akai, daga karfe 10 na safe zuwa karfe 3 na yamma.

• Ka bar sakin jikinka sai wurin da ibadodin Hajji da Umrah suka bukaci a yi hakan.

• Ana ba da shawarar yin amfani da man da ake shafawa don samun kariya daga kunar rana.

Magani:• Ka yi amfani da makunshin kankara da man dansasa jiki.

• Idan bodallan ruwa suka fito a jiki, a guji wasa da su don kar su fashe. Idan suka fashe, a shafa maganin kashe kwayoyin cuta na gida. Amma idan abun ya yi kamari, ka tuntubi likita.

3. Cutar da kwayar Fungi ke haddasawa

Cututtukan Fungi rukunai ne na cututtukan fatar jiki wadanda ke iya haddasa ciwarwata iri daban-daban. Wadannan cututtukan suna yaduwa da yawa a wuraren da ke da yanayin zafi. Daga cikin wadannan cututtuka akwai makero. Makero ciwo ne dake yin gurbi da tambari baki kan fatar jiki, wannan cutar na yaduwa ta hanyar amfani da kayan sawa ko tawul na wanda ya kamu da cutar. Kari kan haka, yawan cinkoson mutane, fitar da gumi mai yawa da yanayin zafi a lokacin aikin Hajji na sa wannan cutar ta yadu a tsakanin mahajjata.

Rigakafi: A tsare yin tsafta. A guji yin amfani da kayan sawa ko tawul din wasu mutane, kuma a rika wanke dukkan ‘yan kanfai da ake amfani da su.

Magani: Ya bambanta gwargwadon irin ciwon da ake da shi. Ana iya amfani da mai, wasu lokutta kuma kwayoyin magani. Amma duk da haka, ya kamata ka tuntubi likita kafin ka sha kowane irin magani.

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 40: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

34 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

34

Raunukan ZafiRaunukan zafi daya daga cikin matsaloli ne da mahajjata ke fuskanta a lokacin da suke gudanar da ibadodinsu. Suna faruwa ne sanadiyyar tsananin zafi lokacin da mahajjata ke tafiya mai yawa suna gumi shabe-shabe.

Ana yawan samun raunukan a wadannan wurare:• Dawafi (zagayen Ka’aba), musamman a lokacin tsakiyar rana. • Sa’ayi (tafiya tsakanin Safa da Marwa), musamman a cikin cinkoson mutane da yanayin zafi mai yawa.• Hawan Arafat da rana tsaka.• Mina (wurin yanka dabbobin hadaya da jifar), saboda tafiya mai nisa da cinkoson mutane.

Ire-iren raunukan zafi:

1. Bugun rana

Bugun rana na nufin kasancewar yanayin zafin jiki kan ma’auni 40ºC na tsawon lokaci. Wannan yanayi ne mai tsanani da tsarin jiki ba zai iya jurewa ba. Juwa da ciwon kai da karewar ruwan jiki na biyo bayan wannan yanayi, kuma kalar fatar jiki ta koma jawur. Idan yanayin zafin jikin bai ragu ba, hankalin marar lafiya zai gushe kuma zai ji ciwon ciki. Kuma zai iya yin amai da gudawa. Idan ciwon ya yi kamari, zai iya samun tsayawar aikin zuciya, jijjigar jiki, ko tsarin jijiyoyin jikinsa ya daina aiki daga karshe ya rasa rayuwarsa.

Bugun rana na bukatar agajin gaugawa, kuma a hanzarta ba marar lafiya wannan taimakon da ke biye:

• A kai marar lafiya wuri mai sanyi.• A cire masa kayan da ke jikinsa kuma a sanyaya jikinsa da ruwan sanyi.• A kai shi wurin da iska ke kadawa, kamar wurin na’urar sanyaya daki ko fanka.• A ba shi abu mai ruwa.• A tunkari assibiti da shi ko a kira motar ba da agajin gaugawa idan ana bukatar hakan.

Page 41: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

35Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 35

2. Takurawar Zafi

Wannan bai kai matsalar bugun rana ba. Alamominsa na bayyana ne da dibgewar jiki a cikin yanayin zafi, hadi da jikewar jiki da sanyin jiki, yin gumi mai yawa, ragewar bugawar zuciya, yin numfashi da sauri, jin kishirwa, ganin juwa, tashin zuciya, dibgewar jiki ko gushewar hankali.

Babban bambanci dake tsakanin takurawar zafi da bugun rana a cikin alamomi shi ne bugun rana na faruwa ne sanadiyyar dagawar yanayin zafin jiki, wadda ita kuma takurawar zafi na faruwa sanadiyyar dibgewar jiki da takura sakamakon zubar da gumin jiki mai yawa da rashin gishirin jiki.

3. Jijjigar jiki da kullewar jijiyoyi

Kullewar jijiyoyi na da matukar zafi. Yana iya faruwa ne a lokacin da ake yin aiki a wuri mai zafi, sanadiyyar rashin isasshin wasu sinadaran da jiki ke bukata wadanda suka zube ta hanyar gumin da aka zubar.

Rigakafin samun raunukan zafi:• A guji daukar lokaci mai tsawo a cikin rana

• Ana ba da shawarar yin amfani da lema da sa sutura mai hasken kala.

• A sha abu mai ruwa (ruwan sha da matsattsen lemu, da sauran su).

• A samu yin bacci isasshe kuma a daina aikin wahala bayan kammala kowace ibada, a duk lokacin da aka samu dama.

Maganin raunukan zafi:Da ganin alamomi, ana ba da shawarar abi wadannan ka’idojin dake biye:

• Dauke marar lafiya daga cikin rana a kai shi wuri mai inuwa.

• Sanyaya jiki ta hanyar cire ma marar lafiya suturar dake jikinsa, kuma a fesa ma jikinsa ruwan sanyi (a kara jikinsa ga na’urar sanyaya daki ko fanka), ko rufe jikinsa da jikakkin kaya.

• Shan maganin rage yanayin zafin jiki ko rage radadin ciwo lokacin da ake bukatar hakan, kafin gushewar hankali.

• A hanzarta kai marar lafiya cibiyar lafiya mafi kusa idan ciwon ya yi kamari, ko a kira motar ba da agaji idan akwai bukatar hakan.

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 42: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

36 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

36

Ciwon SaunkarauLokacin aikin Hajji na daya daga cikin wuraren yaduwar ciwon sankarau, da yake mahajjata sun fito ne daga wurare daban-daban da ake fama da cutar, musamman daga wasu kasashen Afirka. Bayan haka, cinkoson mutane, da matsalar tsafta, da dibgewar jiki na taimakawa wurin yaduwar ciwon sankarau. Wannan ne dalilin da ya sa ciwon sankarau ya zama barazana ga lokacin aikin Hajji.

Ciwon sankarau mafi tsananin kumburin mashinfidin kariyar da ke rufe da kwakwalwa da lakka, wanda aka fi sani da makunshin kwakwalwa da lakka. Yana haddasa mutuwa idan ba a magance shi da wuri ba.

Alamomi:• Zazzabi ko dagawar yanayin zafin jiki • Amai

• Sankarewar wuya • Rashin son haske

• Ciwon kai mai tsanani • Kurajen jiki na bayyana ga yara kanana

• Rudewa ko gushewar hankali • Tambura masu duhu da jajayen kuraje na iya bayyana

Abun da ke haddasa ciwon:Kumburin na iya samuwa ta hanyar kwayoyin cutar virus ko bacteria ko wasu kwayoyin cuta.

Rigakafi:• Allurar rigakafin ciwon sankarau na bayar da kariya ta tsawon kusan shekaru ukku.

• Tsare sharuddan lafiya na kula da tsafta da rage yaduwar cututtukan da ake iya dauka.

• A guji lokuttan cinkoson mutane.

• Samar da hanyoyin shigar iska a cikin gidaje.

• Kebe marar lafiya da kawar da abubuwan da suka fito daga jikinsa.

Page 43: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

37Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 37

Cutar EbolaWannan ciwo ne da ake yadawa mai matukar tsanani, wanda ake zazzabi da zubar da jinni ta cikin jiki. Cutar na matukar kisa. Tana kama mutum da wasu dabbobi, kamar gwaggon biri, bika da birai. Duk da cewar da wuya wannan cutar ta yadu zuwa Saudiyya, ya kamata a dauki matakan tsaro, musamman ga mahajjatan da suke mu’amala da bakin da suka fito daga yankunan da ake fama da cutar a wajen kasar ta Saudiyya.

Yadda cutar ke yaduwa:• Ta hanyar mu’amala da yawunsu, kashinsu ko wasu ruwan dake fita daga jikinsu.

• Cutar ebola na yaduwa ta hanyar mu’amala da mutane ta fasasshiyar fatar jiki ko majina ko jini ko wasu ruwan dake fita daga jikin masu fama da cutar.

• Ta hanyar mu’amala da abubuwan da suka gurbata da ruwan da suka fita daga jikin mai fama da cutar (misali kayan shimfida, sutura, kayan yin aski da allurar da aka yi amfani da ita).

• Jana’izar mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar ta hanyar taba gawarsu ba tare da daukar matakin kariya ba na taimakawa wurin yaduwar cutar Ebola.

Alamomin na fara bayyana daga kwanaki 2 zuwa kwanaki 21 bayan an kamu da kwayar cutar, kuma sukan fito karara cikin kwanaki 8 zuwa kwanaki 10.

Alamomin cutar:• Faruwar zazzabi kwatsam • Ciwon makoshi• Ciwon kai da dibgewar jiki mai tsanani • Ciwon jijiyoyiAbubuwan da za su biyo baya sune; amai, gudawa, kuraje alamomin kasawar koda da aikin hanta, kuma a wani lokacin ana samun zubar jini ta ciki da wajen jiki.

Maganin cutar:Har yanzu ba a samu wani amintaccen maganin kwayar cutar ba. Amma duk da haka, ana daukar wasu matakan magani kamar na rage samun saukin zazzabi, karin ruwan jiki da suka zobe, da kulawa ta musamman idan akwai bukatar yin hakan.

Ko akwai rigakafin cutar?Har yanzu babu wani magani ko rigakafin da aka amince da shi, kuma cibiyoyin bincike da dama na aiki don yin magani da rigakafin cutar.

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 44: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

38 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

38

Matakan kariya da rage yaduwa:• Tsare tsaftar jiki da ta muhalli, wanda ya hada da wanke hannuwa da kyau da ruwa da sabulu, ko da ruwan sinadarin

kashe kwayoyin cuta, akai-akai, musamman: bayan an fito bandaki, bayan an taba wurare da kayan da suka gurbata da ruwan da suka fito daga jikin mai fama da cutar, kafin ci da bayan cin abinci ko sarrafa shi, bayan yin tari ko atishaya.

• Rage hatsarin yaduwar cutar daga dabbobi zuwa mutane, ta hanyar kauce ma yin mu’amala da jemage, ko birai dake yankin da ake fama da cutar.

• A dafa jini da naman dabbobi da kyau kafin a ci.• A guji mu’amala da mutanen dake da alamomin kamuwa da cutar Ebola, musamman da kayan kula da tsaftarsu irin

tawul, asaken aski, kofunan shan ruwa da cokullan cin abinci. • A yi amfani da safar hannu da kayan kariyar da suka dace a lokacin da ake shirya jana’izar mutanen da cutar ta

kashe, kuma a rufe su nan take.• Bin dokokin da Ma’aikatar Lafiya ta tsara.

Dibgewar Jijiyoyi da girtsiWasu mahajjata na iya samun dibgewar jijiyoyi da girtsi sanadiyyar yawan tafiye-tafiye lokacin da suke gudanar da ibadodi.

Alamomi:Tsananin dibgewar jijiyoyi ya bambanta, ya danganta da irin karfi da lafiya da kuma yawan zirga-zirgar mahajjaci:

• Dibgewar girtsi: Alamomin sun bambanta, tsakanin jin radadi da kumburi ko ‘yar yagewar girtsi ko yagewarsa baki daya.

• Dibgewar Jijiyoyi: Alamomin sun bambanta, tsakanin jin radadi da kullewar jijiyoyin da zai kai ga yagewar jijiya kadan ko yagewa mai tsanani.

Idan wasu alamomi suka bayyana, a tunkari assibiti, wurin da Ma’aikatar Lafiya ta tanadi ayukkan kula da lafiya kyauta ga mahajjata.

Page 45: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

39Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 39

Abun da ke haddasa dibgewar Girtsi da Jijiyoyi:• Rashin lafiyar motsa jiki`

• Yin aikin gajiyarwa

• Dagewa da yin tafiya da karfi

Magani:• Ka bar tafiya da zarar ka ji wani radadi.

• Ka lunda wurin da abun ya shafa don rage radadi da hana taruwar jini. Kuma ka na iya daure wurin da bandeji, a zagayen jijiyar da abun ya shafa. Ana samun irin wadannan bandejin a shagunan sayar da magani.

• Ka sanyaya wurin raunin da kankara ko ruwan sanyi don rage radadi.

• Ka daga wurin da ke da raunin sama don rage kumburi; a lokacin da kake bacci ko zaune a gida.

• Ka tuntubi likita idan akwai bukatar hakan.

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 46: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Mata da Yara a lokacin aikin Hajji da Umrah

Aikin Hajji tafiya ce mai wahala dake bukatar babban kokari. Kuma mata nada nasu matsayi a lokacin aikin Hajji; suna iya kasancewa da juna biyu, samun jinin al’ada ko wahala saboda halittarsu ta rashin juriya.

Lokacin Jinin Al’ada:Idan maccen da za ta tafi wurin aikin Hajji na son ta sha kwayoyin hana zubar jinin al’ada don ta gudanar da aikin Hajji da kyau, sai ta bi wadannan matakan masu zuwa:• Ki tuntubi likitan mata kafin ki tafi aikin Hajji cikin isasshen lokaci; akalla kwanaki 7 ko yadda likitan mata ya ba da

shawara. • Ki tabbatar da yadda za ki sha kwayoyin, da yawan kwayoyin da za ki sha cikin kayyadadden lokaci kamar yadda

likitan mata ya shawarce ki.• Akwai wasu matsaloli tare da wadannan kwayoyin da suka hada da tashin zuciya, ciwon kai, radadi a kewayen

mama, da jin rashin son zama kurum.

Mata Masu Juna Biyu da aikin Hajji:

Ana ba da shawara ga mai juna biyu da ta daga zuwa aikin Hajji. Amma duk da haka, idan har sai mai juna biyu ta yi aikin Hajji don wasu dalilai, muna ba ta shawarar bin wasu matakan kariya don kauce ma hatsarorin da ka iya zama barazana ga masu juna biyu da tayin dake cikinsu saboda takurawa. Ga hatsurran da ake iya samu:• Haihuwa ba lokacin ta ba.• Maiyiwuwa ne jariri ya bukaci kulawa ta mussamman da zarar an haife shi.• Maiyiwuwa ne ta samu kasadar kamuwa da wasu cututtukan da ake yadawa saboda rashin garkuwar jiki da

cinkoson mutane.

Page 47: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

41Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 41

Ya kamata mai juna biyu ta daga zuwa aikin Hajji don wadannan abubuwan dake biye:• Tarihin haihuwa ba lokacin ta ba.• Yin bari.• Samun ciwon sugan juna biyu.• Ciwon zuciya da hawan jini ko ciwon koda da sauran su. • Zubar jinin ciki• Kasancewar mahaifa kasa-kasa mai makon zaman ta sama

Matakan Lafiya don Mai Juna Biyu:• Ki tuntubi likitan haihuwar da ke kula da ke don jin ko za ki iya yin aiki ba tare da samun wata matsala ba. • Ki tuntubi likitan haihuwa ki ji ko za ki iya karbar rigakafin ciwon sankarau da mura kafin akalla kwanaki goma na

fara aikin Hajji.• Ki tabbatar da kin zo da duk magungunan da kike bukata kuma wadanda za su ishe ki na tsawon lokacin aikin Hajji.

Matakai don kiyayewar mai juna biyu a lokacin tafiya:• Ki sha ruwa da yawa.• Ki rika tafiya ta dan lokaci a duk bayan sa’a daya ko sa’a biyu don kauce ma samun taruwar jini ga kafafu. • Ki yi tafiya bayan kowace sa’a daya ko sa’a biyu a cikin jirgin sama ko motar safa. Idan kina tafiya ne da motar gida

direba ya rika tsayawa duk bayan sa’a biyu don ki dan yi tafiya.

Mai juna biyu ta guji shiga cinkoson mutane kuma ta zabi lokuttan da suka dace ta gudanar da ibadodi don kauce ma matsewar mutane.

Idan akwai bukatar gaugawa sai a kira wan-nan lambar wayar 911

Page 48: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

42 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

42

Matakai don Mata Masu Juna Biyu Lokacin aikin Hajji:Mai juna biyu na iya samun karancin ruwan jiki saboda yawan amai musamman a lokacin wata daya na juna biyun, a lokacin ne za ta iya yin barin ciki saboda dibgewar jiki da cinkoson mutane. Don haka mata masu juna biyu su kula da wadannan abubuwan dake biye:• Ki guji shiga wurin da za iya matse maki jiki.• Ki tabbatar da kin sa kaya da takalmin da suka dace.• Ki sha ruwa da yawa kuma ki guji wurin da ke da yanayin zafi mai yawa.• Ki yi tafiya ta dan lokaci bayan kowace sa’a daya ko sa’a biyu don kauce ma samun kumburin kafafu.• Idan kika ji zuwan jini, ciwon ciki, matsanancin ciwon kai ko yanayin zafi mai yawa, ki tafi cibiyar lafiya mafi kusa ko

assibiti. • Ki guji kokarin yin wani abunda yafi karfinki, kuma ki yi amfani da damar da aka amince da ita idan bukatar hakan

ta taso, kamar amfani da keken guragu a wurin Dawafi (zagayen Ka’aba da yin Sa’ayi) a lokacin da kike jin kasala.

Jarirai da Yara a lokacin aikin Hajji:Ana ba da shawarar cewa kar a tafi da yaran da ba su balaga ba wurin aikin Hajji saboda wadannan dalilai: • Yara sun fi samun kasadar kamuwa da cututtuka irin su matsalar numfashi da ta narkewar abinci ko gudawa da

amai. • Yara sun fi samun kasadar karewar ruwan jiki fiye da manya maiyiwuwa ne saboda yanayin zafi mai yawa ko shan

ruwa kadan da suke yi. • Takurawar rana na gajiyar da yara a lokacin aikin Hajji wanda kuma ke hana su son cin abinci; wanda zai haifar masu

da rashin ruwan jiki. • Yara na iya bacewa saboda cinkoson mutane a lokacin aikin Hajji.

Mai juna biyu ta hanzarta zuwa cibiyar lafiya mafi kusa ko assibiti idan ta ji daya daga cikin wadannan alamomin: • Zubar jinni, fitar wani abu daga farji wanda ba a saba gani ba• Matsanancin ciwon ciki• Matsanancin ciwon kai da gani buji-buji

Page 49: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

43Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah 43

Matakan da ya kamata Uwaye su sani idan za su zo da yaransu:• A sa ma hannun yaro munduwa mai nuna cikakken suna, wurin zama, lambar waya da

kuma sunan tawaga.

• A tabbatar da yaro ya karbi muhimman alluran rigakafi, kuma a tambayi likita game da sauran alluran rigakafin.

• Yaro ya sha ruwa masu yawa don kauce ma bushewar ruwan jiki.

• Yaro ya rika wanke hannuwa akai-akai.

• A tabbatar da tsaftacewa da tsane tsakanin cinyoyin yaro don kariya daga banbarewar fatar jiki.

• A tabbatar da tsaftar abinci.

• A yi kokarin kauce ma zuwa da yara wurin cinkoson mutane.

• Ana ba da shawarar a tafi wurin likita idan aka samu matsalolin lafiya, kamar gudawa, amai da canjin yanayin zafin jiki.

Idan yaranka sun bi ka zuwa wurin aikin Hajji, ka tabbatar da ka ba su muhimman alluran rigakafi, kari kan sauran rigakafin da ake yi na aikin Haji.

Page 50: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

44 Lafiyar jikinku a lokacin gudanar da aikin Hajj & Umrah

44

Alamomin da ke biyo Bayan Kammala aikin Hajji

Wasu mahajjata na samun wasu alamomi bayan sun kammala aikin Hajji. Wadanda za a iya kira matsalolin bayan kammala aikin Hajji. Alamomin ba cuta ba ce, amma tarin wasu alamomi ne da suke shafar mahajjata a lokacin da suke gudanar da ibadodin Hajji, kamar gajiya, ciwon jiki, rashin isasshen bacci, da sauran su. Amma wadannan alamomin za su bace da wuri ta hanyar shan maganin kashe radadi. Wadannan alamomin sun hada da:

• Gajiya, kasala da dibgewar jiki;

• Ciwon jijiyoyi da ciwon jiki;

• Ciwonkai da gabobi;

• Duhun fatar jiki;

• Sanyi;

• Da kuma yawan bacci.

Kuma ana samun wadannan alamomin sanadiyyar:

• Yawan zama cikin rana;

• Yawan tafiye-tafiye;

• Da kuma kamuwa da ciwon sanyi da mura.

Kamar yadda muka yi bayani tun farko, wadannan alamomin za su bace a cikin lokaci, ta hanyar hutawa da shan maganin kashe radadi. Idan har alamomin suka yi muni ko suka cigaba na tsawon lokaci, ka nemi shawarar likita.

A lokacin da aka dawo gida, mahajjaci ya guji haduwa da wasu mutane idan ya kamu da sanyi, mura da sauran su, kuma ya tafi wurin likta idan alamomin sun yi muni.

Page 51: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Manazarta

1. Yanar gizon Ma’aikatar Lafiya ta gwamnatin Kasar Saudiyya

www.moh.gov.sa

2. Hukumar Lafiya ta Duniya

www.who.it

3. Cibiyar Kiyayewa da Hana Yaduwar Cututtuka ta Turai

www.eurosurveillance.org

4. Kundin bayanai kan sha’anin Lafiya da aka buga cikin Harshen Larabci na Sarki Abdullah bin Abdulaziz

www.kaahe.org

5. Cibiyoyin Kiyayewa da Hana yaduwar Cututtuka

www.cdc.gov

6. Ayukkan Lafiya na Kasa (NHS)

www.nhs.uk

Page 52: Babban Jagora don Lafiyar - MOH · A lokacin da aka yi dogon zama cikin jirgi ko mota, ana son mutum ya dan yi tafiya ko ya mike tsaye na dan wani lokaci bayan ko wace sa’a daya

Ma’aikatar Lafiya

Bugu na Ukku1438H (2017G)