64
Littafi don Makarantun Firamare na 4 Hasken Karatu Adamu A. Kiyawa Tijjani S. Almajir Halima A. Îangambo Sani L. Abdurrahman Hausa prel 4.indd 1 9/11/14 8:43 AM

Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

  • Upload
    others

  • View
    105

  • Download
    78

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

i

Littafi don Makarantun Firamare na 4

Hasken Karatu

Adamu A. KiyawaTijjani S. AlmajirHalima A. ÎangamboSani L. Abdurrahman

Hausa prel 4.indd 1 9/11/14 8:43 AM

Page 2: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

ii

Learn Africa PlcFelix Iwerebon House52 Obå Åkrån ÅvenueP.M.B. 21036Ikejå, Lågos StåteTel. (01) 7403967, 4393111Fåx (01) 4964370E-måil: [email protected]: www.learnafricaplc.com

Åreå offices ånd brånchesÅbujå, Ajegunle, Åkure, Benin, Enugu, Ibådån, Ilorin, Jos, Kåno, Onitsha, Owerri, Port-Harcourt, Zåriå ånd representåtives throughout Nigeriå

Åll rights reserved. No pårt of this publicåtion måy be reproduced, stored in å retrievål system, or trånsmitted in åny form or by åny meåns, electronic, mechånicål, photocopying or otherwise, without the prior permission of Learn Africå Plc.

© Learn Africa Plc 2014First published 2014

ISBN 978 978 925 102 5

Illustråtions by Franklin Oyekusibe

Hausa prel 4.indd 2 9/11/14 8:43 AM

Page 3: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

iii

Abubuwan da ke Ciki

Babi Shafi1 Al˚aluman˚idaya(51-100) 1 Jerinalkaluman˚idaya 1 Aiki 2 Jagora 2

2 Insha'in baka I 3 Guntun gatarinka 3 Tambayoyi 4 Jagora 4

3 Insha'inbakaII 5 Falke da birai 5 Tambayoyi 6 Jagora 6

4 Taifod da kwalara 7 Taifod 7 Tambayoyi 8 Jagora 8

5 Zazza∫inmaleriya 9 Tambayoyi 10 Jagora 10

6 Gabatardarubutunwasi˚a 11 Ma'anarwasi˚a 11 Muhimmancinwasi˚a 11

Hausa prel 4.indd 3 9/11/14 8:43 AM

Page 4: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

iv

Aiki 14 Tambayoyi 15 Jagora 16

7 Farakoyenka'idojinrubutu 17 Manyanba˚a˚e 17 ˚anananba˚a˚e 17 Manyanda˚anananwasula 17 Wurarendaakeamfanidamanyanba˚a˚e 18 Wurarendaaketashidakaraminba˚i 20 Tambayoyi 20 Aiki 21 Jagora 22

8 Gajerunwasanninkwaikwayo 22 Wasan kwaikwayo cikin tashe 22 Na maza 22 Na mata 23 Tambayoyi 24 Jagora 25

9 Gajerunwakoki 26 Wa˚arbiniyaye 26 Muhimman kalmomi 28 Aiki 28 Tambayoyi 29 Jagora 29

10 Kacici-kacici 30 Misalan kacici-kacici 31 Tambayoyi 31 Aiki 32 Jagora 32

Hausa prel 4.indd 4 9/11/14 8:43 AM

Page 5: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

v

11 Karinmaganadamaganganunazanci 33 Ma'anar karin magana 33 Misalan karin magana 33 Aiki 34 Maganganun azanci 34 Jagora 37

12 Aure 39 Biki 39 Aiki 41 Tambayoyi 41

Jagora 42 13 Hausawa da sana'o'insu 43 Ma'anar sana'a 43 Bayanin wasu sana'o'in Hausawa 43 Muhimmancin sana'o'i 46 Tambayoyi 46 Aiki 47 Jagora 47

14 Abincin Hausawa 48 Ga yadda rabe-raben abincin Hausawa yake 48 Muhimmancin abinci 50 Aiki 50 Tambayoyi 52 Jagora 52

15 TufafinHausawa 53 Tufafin maza 53 Tufafin mata 55 Tambayoyi 56 Aiki 57 Jagora 57

Hausa prel 4.indd 5 9/11/14 8:43 AM

Page 6: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

vi

Gabatarwa

An rubuta jerin wannan littatafi guda shida mai suna Hasken Karatudonakoyawa∂alibai

namakarantunfiramaredagashekarata∂ayazuwatashida.Anrubutadarussanda

zaakoyartabinsabuwarmanhajarHausawaddaHukumarBincikedaHa∫akaIlimita

Nijeriya(NERDC)tashirya.Darussandakecikinwa∂annanlitattafaisunshafifannonin

nahawudaadabidaal’adunHausawa.Anyiamfanidahanyoyisau˚a˚awajentaimakon

koyardawa∂annanlitattafaicikinsau˚i.Wa∂annanhanyoyisunha∂ada:

1 Akwai shiryayyun tambayoyi, masu sa a karanta darasi, a fahimce shi sosai kafin

bayar da amsoshin.

2 Akwaizanenhotuna,daalamominrubutu,adukwurindayakamata,don˚ara

armasa karatu da ilimantarwa, musamman don gane abubuwan, da ake bayani

sosai.

3 Akwai jagora a karshen kowane babi, don baiwa malami haske game da yadda

zaigudanardakoyarwa,dakuma˚arinhaskecikinwasulitattafan.

Anafatanidan∂alibiyagamawa∂annanlitattafaigudashida,tozaisamicikakkiyar

shimfi∂atafahimtarfanninHausa.Donhaka,muhimmiyarmanufarwannanlittafi,ita

cesamarwamalamaiabubuwandazasukoyarcikinsau˚i,sukuma∂alibaisuga

darussan da ake koya masu a zahiri. Allah ya taimake mu, amin.

Hausa prel 4.indd 6 9/11/14 8:43 AM

Page 7: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

1

Babi na 1

Al˚aluman ˚idaya (51–100)

Jerin alkaluman ˚idaya

A wannan babi za a dubi ˚idaya ne, daga hamsin da ∂aya har zuwa ∂ari. A nan za

a kawo yadda ake fa∂arsu da Hausa, daga baya kuma a kawo yadda ake rubuta su,

da lambobi don tantancewa.

Wannan ˚idaya itace kamar haka:

Hamsin da ∂aya 51

Hamsin da biyu 52

Hamsin da uku 53

Hamsin da hu∂u 54

Hamsin da biyar 55

Hamsin da shida 56

Hamsin da bakwai 57

Hamsin da takwas 58

Hasin da tara 59

Sittin 60

Sittin da ∂aya 61

Sittin da biyu 62

Sittin da uku 63

Sittin da hu∂u 64

Sittin da biyar 65

Sittin da shida 66

Sittin da bakwai 67

Sittin da takwas 68

Sittin da tara 69

Saba’in 70

Saba’in da ∂aya 71

Saba’in da biyu 72

Saba’in da uku 73

Saba’in da hu∂u 74

Saba’in da biyar 75

Saba’in da shida 76

Saba’in da bakwai 77

Saba’in da takwas 78

Saba’in da tara 79

Tamanin 80

Tamanin da ∂aya 81

Tamanin da biyu 82

Tamanin da uku 83

Tamanin da hu∂u 84

Tamanin da biyar 85

Tamanin da shida 86

Tamanin da bakwai 87

Hausa Pry 4.indd 1 9/11/14 8:44 AM

Page 8: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

2

Tamanin da takwas 88

Tamanin da tara 89

Casa’in 90

Casa’in da ∂aya 91

Casa’in da biyu 92

Casa’in da uku 93

Casa’in da hu∂u 94

Casa’in da biyar 95

Casa’in da shida 96

Casa’in da bakwai 97

Casa’in da takwas 98

Casa’in da tara 99

Îari 100Aiki

A Rubuta wa∂annan lambobi da Hausa.

52 _________ 68 _________ 86 _________ 94 _________

57 _________ 74 _________ 88 _________ 100 _________

60 _________ 79 _________ 92 _________ 96 _________

B Cike guraben da aka bari da abin da ya dace na kalmomin ˚idaya.

Hamsin da shida

71

Sittin

64

Tamanin da biyu

Casa’in da biyar

51

Îari

Sittin da bakwai

99

Jagora

Malami ya auna fahimtar yara ta hanyar rubuta wa∂ansu lambobi a kan allo,

sannan ya tambaye su su fa∂i sunayen wa∂annan lambobi ko adadinsu.

Hausa Pry 4.indd 2 9/11/14 8:44 AM

Page 9: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

3

Babi na 2

Insha’in baka I

Insha’ i ya ˚unshi gajerun labarai, ko jawabai wa∂anda ake rubutawa a kan wani abu

ko wata magana. Insha’i kan kasance dogo ko gajere. Ana rubuta insha’i, sannan

tambayoyi su biyo baya.

Guntun gatarinka

A wani gari wai shi Zairawa, an yi wani mutum da ake kira Hari˚u. Hari˚u mutum ne

kamili, wanda ya san ya kamata. Babu wanda zai ce ya ta∫a ganin wanda suka yi

kace-nace da shi. Ko da yake Hari˚u ba mai wadata ba ne, duk da haka wannan ba

ta ∂a∂a shi da ˚asa ba. Kullum idan ya yi sallah yakan gode wa Allah, ma∂aukakin

Sarki da ya wadata shi da lafiyar da zai je ya nemi na kansa . Bai ta∫a nuna gazawarsa

wajen ˚o˚arin nema wa iyalinsa abin da za su ci ba. Wani abin ban sha’awa kuma, shi

ne yadda Allah ya sanya fahimtar juna tsakaninsa da matarsa. Duk irin abin da Hari˚u

ya shigo da shi gida,matar ba ta ta∫a raina masa ba. A kodayaushe tana ˚arfafa masa

gwiwa, tana yi masa addu’ar fatan alheri.

Shazali shi ne ∂a ∂aya tilo, da Allah ya arzurta hari˚u da matarasa da shi. Allah

mai yin yadda ya so. Duk da irin halin kirki na wa∂annan mutane, ba su dace da ∂a na

kirki ba. Shazali ba shi da wurin zuwa, in ban da gidan sinima, da yawo a tashar mota,

shi ne dandalin ‘yan caca da gidan karuwai. Ba ma a nan ta tsaya ba, domin ba a yin

kwana uku ba a ji kansu da wani ba. Wannan irin hali nasa, ya sa idan mutane suka

ha∂u da shi a kan hanya, sai sukan ratse don kada ya banke su. Sukan ce, ‘Albasa ba

ta yi halin ruwa ba’. Babu irin nasihar da ubansa bai yi masa ba, amma sai ya zama

kamar da∂a tura shi ake yi. Haka ubanya dangana, ya zura masa ido.

A kwana a tashi, sai Shazali ya ƙulla abota da Shargalle. Shi ∂an wani attajiri ne

da ke kusa da gidansu. Karshen abin dai, har ya tare gidan su Shargalle. Su ci, su

Hausa Pry 4.indd 3 9/11/14 8:44 AM

Page 10: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

4

sha,su ɗaura tare,ya zama kamar ɗan gidan. Ya ƙi iyayensa ƙiri da muzu, suna ji suna gani,sai ka ce ba su suka haife shi ba. Ga su kuma baki da hanci. Abinka da duniya, sai rannan wata irin masassara ta kama shi, ya kumbura kamar taiki. Aka yi ta magani, amma ina! Aka kira wani boka, ya yi kasada ya kunna kai inda Shazali yake. Ai nan take ya fito a gigice, yana cewa shi kam, ba zai iya yi masa magani ba. Domin wannan ciwo irin wanda ake ɗauka da sauri ne, kuma mai wuyar magani. Da jin haka, sai Attajirin ya umarci bayinsa da su fitar da shi daga gidan, su mayar da shi gidansu. Aka kwashe shi haka nan a ƙyamace, aka kai wa iyayensa, aka jibge musu. Su kuma suka ci gaba da nema masa taimako, suna tattalinsa tare da nuna tausayi. Uwa kuka uba kuka. Allah kuwa ya taimake su, ya samu warkewa sarai. Ya samu lafiya, ya yi sumul, ya mai da jiki. Daga nan ya yi hankali, ya dangana da inda Allah ya ajiye shi.

Tambayoyi1. Yaya sunan mahaifin Shazali?2. Shin Shazali ya gaji halin mahaifinsa?3. Da wa Shazali ya ˚ulla abota?4. Mene ne ya kumbura Shazali?5. Shin halin Shazali abin koyi ne?6. Shazali ba shi da wurin zuwa sai _________________ . a) coci b) kasuwa c) masallaci d) sinima 7. Mutane ka _________________ . a) ratse b) gudu c) zanna d) tafi8. Babu irin ____________ da ubansa bai yi masa ba. a) dukan b) nasihar c) zagin d) yabon9. Shazali ya ˚ulla abota ne da ˚undalo. a) Ee b) A’a10. Matar Hari˚u ba ta yi masa biyayya. a) Ee b) A’a

Jagora

Malami ya amarci yara su karanta wannan insha’i a cikin aji, sa annan su amsa

tambayoyin da ke biye ba tare da bu∂a littafi ba.

Hausa Pry 4.indd 4 9/11/14 8:44 AM

Page 11: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

5

Insha’in baka II

Falke da birai

An yi wani falke mai sayar da huluna. Wata rana ya tafi kasuwar wani ˚auye, da

hulunansa. Yana cikin tafiya sai ya ga wata bishiya mai inuwa, ya ratse gindin bishiyar

nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna

da wata ‘yar dabara, ya ∂aure duk hulunan nan a kansa, wato ya yi maganin ∫arayi

ke nan. Da sanyin inuwa ya kwashe shi, sai ya yi ta barci har da minshari, kamar yana

kan gadonsa. Îaurin da ya yi wa hulunan ya kwance bai ankara ba.

Babi na 3

Hausa Pry 4.indd 5 9/11/14 8:44 AM

Page 12: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

6

Zuwa can sai wa∂ansu birai, suka biyo ta inda falken nan yake barci. Da suka

tabbata barci yake yi, sai ∂ayansu ya la∫a∫a ya zare hula ∂aya, ya sa a kansa. Sauran

birai da suka ga haka, su ma sai suka kwaikwayi ∂an’uwansu, kowa ya ∂auki hula

guda ya ∂ora a kansa. Suka hau kan bishiya, suka bar falke da tsohuwar hularsa a ka

kawai. Falke ya farka bai ga hulunansa ba. Ya duba gabas da yamma, kudu da arewa

bai ga kowa ba. Da ya ∂aga kai sama, sai ya yi arba da ∫arayinsa a kan itace,wato

biran nan. Ya yi juyin duniyar nan suka ˚i ba shi hulunansa. Haushi ya kama shi, ya

cire hular da ke kansa, ya jefar don haushi. Nan da nan sai birai suka sauko daga kan

bishiya, suka kewaye shi. Suka yi ta jefar da nasu hulunan a ˚asa. Falke ya tsince

hulunansa, ya tafi kasuwa abinsa.

Tambayoyi

1. Ina falke ya dosa?

2. A ina falke ya ratse don ya huta?

3. Wace dabara falke ya tuna?

4. Su wanene ∫arayin falke a wannan labarin?

5. Shin magiyar falke ce ta sa ya samu hulunansa?

6. Me falke yake sayarwa?

a) Riguna b) Takalma c) Huluna

7. Falke ya tafi ______________ da hulunansa.

a) kasuwar wani ˚auye b) unguwarsu c) ˚auyensu

8. Su wane ne suka kwashe hulunan falke lokacin da yake barci?

a) Giwaye b) Birai c) Karnuka

Jagora

Malami zai jagoranci ∂alibai, wajen karanta wa∂annan labarai da aka kawo.

Malami ya sanya ∂alibai, su amsa tambayoyin da aka bayar a ˚arshen kowane

labari. Malami na iya nemo wasu labarai, daga cikin littattafan labarun gargajiya

don karantawa ∂alibai.

Hausa Pry 4.indd 6 9/11/14 8:44 AM

Page 13: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

7

Taifod da kwalara

Taifod

Cutar taifod tana samuwa ne, sanadiyyar wasu ˚wayoyin cututtuka da suke samuwa,

ta hanyar shan gur∫ataccen ruwa, ko abinci marasa tsafta ko wanda ya lalace. Akwai

muhimman dalilai da ke kawo wanna cuta da suka ha∂a; shan gur∫ataccen ruwa ko

cin ru∫a∫∫en abinci da wanda ˚ura ta hau. Haka nan, akwai barin ruwan sha a bu∂e

ko rashin tsabtace shi, da rashin wanke ganyayyaki da ‘yayan itatuwa kafin a ci, da

kuma rashin wanke hannu bayan fitowa daga bayan gida. Bayan nan, wani dalilin da

ke kawo ciwon shi ne rashin tafasa ruwan rijiya, da na Kogi kafin a sha, sai rashin

tsaftace kayan dafa abinci da na girki.

Akwai hanyoyi da dama da mutum zai iya bi, don kare kansa daga wa∂annan

cututtuka kamar; tabbatar da tsaftar abin da za a ci, da wanke ganyayyaki da gishiri da

tsaftace hannu kafin da kuma bayan an ci abinci. Sai kuma killace abinci daga wari.

Babi na 4

Hausa Pry 4.indd 7 9/11/14 8:44 AM

Page 14: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

8

Cutar kwalara kuwa, ita ce wadda aka fi sani da amai da gudawa. Yawanci ˚udaje

ne suke ya∂a ta. Mutumin da ya kamu, yana yin amai da gudawa akai-akai. Abubuwa

da ke kawo wannan cuta, sun ha∂a da; yin ba-haya a ko’ina, rashin share makewayi

da zuba maganin ˚wari, sai kuma rashin rufe abinci.

Kamar cutar taifod, kwalara ma akwai hanyoyin magance ta kamar haka; kawar

da ˚azanta daga gidaje da rurrufe abinci sosai da dafa abinci sosai, don ˚wayoyin cuta

su mutu da kuma guje wa yin ba-haya a ko’ina.

Tambayoyi

1. Kawo abubuwa uku da suke kawo cutar taifod?

2. Shin wace cuta ce ˚udaje ke ya∂awa?

3. Wace irin cuta ce ke sa mutunm amai da gudawa?

4. Wace irin cuta abincin da ya lalace ke haddasawa?

5. Kawo hanyoyi biyun da mutum zai kare kansa daga kwalara.

6. wayoyin taifod kan samu ta hanyar shan ________ ruwa.

a) tsaftataccen b) gur∫ataccen c) rinannen d) killataccen

7. Rashin wanke ganyayyaki da ________kafin a ci kan haifar da cutar taifod.

a) ˚afa b) Itatuwa c) bishiyoyi d) gishiri

8. ________ da gudawa ne ke kama mai cutar kwalara.

a) Amai b) Zazza∫i c) Atini d) Ciwon kai

9. Yin ba-haya a ________ kan jawo cutar kwalara.

a) ban∂aki b) ko’ina c) gona d) makaranta

10. Idan an dafa abinci sosai ˚wayoyin cuta kan rayu.

a) Ee b) A’a

Jagora

Malami ya jagora yara wajen karata wannan babi.Yara su amsa tambayoyin da

suke biye ba tare da buda littafi ba. Malami ya yi wa yara karin bayan game da cutar

taifod da kwalara.

Hausa Pry 4.indd 8 9/11/14 8:44 AM

Page 15: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

9

Zazza∫in maleriya

Mene ne zazzabin maleriya?

Zazza∫in maleriya zazza∫i ne mai zafi da sauro yake haddasawa ta hanyar cizon

mutane. Sauro yana zuba wa mutane ta hanyar zu˚ar jininsu. Ta haka ne yake iya

ya∂a kwayoyin cuta a jiki. Idan mutum ya kamu da wannan zazza∫i, jikinsa yakkan

∂auki zafi, ya ri˚a karkarwar sanyi.

Babi na 5

Babban abin da ke kawo zazza∫in maleriya, shi ne sauro. Akwai abubuwa da dama

da ke kawo yawaitar sauro a muhallanmu, wa∂anda su ne ke jawo zazza∫in maleriya.

Wa∂annan abubuwa su ne kaman barin ruwa ya taru a bayan ∂akunanmu, da jibge

shara a gida da rashin share makewayi, da rashin share gida da tsaftace shi da barin

juji a kewayen muhalli, da barin ciyayi ko’ina, da rashin yashe magudanan ruwa da dai

sauransu.

Hausa Pry 4.indd 9 9/11/14 8:45 AM

Page 16: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

10

Babban abin da ke hana ya∂uwar maleriya, shi ne hana sauro ya∂uwa, da hana shi

shiga ∂akunanmu ta hanyoyi irin su, yin amfani da gidan sauro, da yin feshin magani,

da share sa˚o da lungunan da sauro ke iya ∫uya, da hana taruwar ruwa a kewayen

muhallinmu, da ˚one juji tare da zubar da shi da tsaftace makewayi, da wurin wanki da

wajen wanke-wanke, da kuma nome ciyayin da ke kewaye da muhalinmu.

Tambayoyi

1. Me yake jawo zazza∫in maleriya?

2. Wacce babbar alama ce ke nuna kamuwa da zazza∫in maleriya?

3. Kawo hanyoyi biyu na riga-kafin cutar maleriya.

4. Kawo dalilai biyu da ke jawo ya∂uwar sauro.

5. Kawo hanya guda ∂aya da ke hana sauro shiga ∂akunanmu.

6. Jikin mutum kan ∂auki ________ idan ya kamu da zazza∫in maleriya.

7. ________ ne babban abin da ke kawo zazza∫in maleriya

a) Kwatami b) uda c) Sauro d) Zafi

8. Hana taruwar ________a muhallinmu na hana ya∂uwar sauro.

a) kyankyaso b) ciyawa c) ˚uda d) yanar gizo

9. uda kan taimaka wajen ya∂a cutar zazza∫in maleriya.

a) Ee b) A’a

10. Barin kwatami a gefen gida na jawo ya∂uwar sauro.

a) Ee b) A’a

Jagora

Malami ya jagoranci yara wajen karanta wannan babi. Yara su amsa tambayoyin

da suke biye ba tare da bu∂a littafi ba. Malami ya yi wa yara karin bayani game

da hanyoyin ya∂uwar sauro da hanyoyin magance hakan.

Hausa Pry 4.indd 10 9/11/14 8:45 AM

Page 17: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

11

Babi na 6

Gabatar da rubutun wasi˚a

Ma’anar wasi˚a

Wasi˚a hanya ce ta aika wa da sa˚o a rubuce.

Muhimmancin wasi˚a

a) Akan rubuta wasi˚a, don aikawa da gaisuwa ko kuma wani sa˚o na musamman.

b) Akan iya ˚ulla wani ciniki ko wata harkar arziki ta wasi˚a.

c) Akan iya sanar da wasu mutane da ke nesa, labarin garinsu ko ˚asarsu.

d) Wasi˚a ta fi sa˚on baki, saboda ita babu ˚ari ko ragi a cikin maganar kuma babu

mantuwa.

Akwai wasu abubuwa muhimmai, da ya kamata wasi˚a ta kasance tana da su.

Wa∂annan abubuwa sun ˚unshi:

1. Adireshi: Shi ne lambar gida da, sunan layi, da sunan unguwa, da lambar

akwatin gidan waya, da sunan jiha da kuma kwanan wata.

2. Gabatarwa: Shi ne fara wasi˚a, ta hanyar gaisar da mutumin da ake rubutawa

wasi˚ar.

3. Gangar jiki: Shi ne inda mai rubuta wasi˚a, zai yi bayanin sa˚on da wasi˚a take

∂auke da shi da dalilin rubuta wasi˚ar.

Hausa Pry 4.indd 11 9/11/14 8:45 AM

Page 18: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

12

d) Kammalawa: Shi ne ˚arshen wasi˚a, wato inda mai rubuta wasi˚a zai yi sallama

da mutumin da yake rubuta wa wasi˚ar.

Ga wata wasi˚a da Samir ya rubuta wa abokinsa Hassan, da ke karatu a wata

makarantar kwana.

Kwalejin Gwamnati Ta Kukawa,

Akwatin Gidan Waya 990,

Kukawa.

5 ga Maris, 2011 kwanan wata

Zuwa ga abokina Hassan,

Gaisuwa mai tarin yawa da so da yarda. Ina fata kana cikin ˚oshin lafiya tare

da sauran abokan karatu, amin.

Bayan gaisuwa, na rubuto maka wannan wasi˚a ne, domin in tambayi lafiyarka

da ta sauran abokan karatunka. Ka san mun da∂e ba mu ha∂u ba. Tun da ka

koma bayan hutu ban sake ji daga gare ka ba. Bayan tafiyarka, shin ka kuwa

sami labarin cewa babanka ya sake sabuwar mota fil. Yanzu ana cewa ma duk

unguwar babu mota irinta. Ina kuma fata kana karatu sosai, kamar yadda nake

yi. Ina jira in ji daga gare ka. Wassalam, ka huta lafiya.

Ni ne naka har kullum,

Samir Abdullahi.

Adireshi

Gab

atar

wa

Gan

garji

ki

}}}

}

Rufewa

Hausa Pry 4.indd 12 9/11/14 8:45 AM

Page 19: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

13

Bayan samir ya rubuta wa abokinsa Hassan wasi˚a, sai Hassan ya rubuta masa tasa

wasi˚ar kamar haka:

Makaratar Sakandaren Gwamnati ta Malamawa,

Akwatin Gidan waya 244,

Malamawa.

15 ga Maris, 2011

Zuwa ga abokina Samir,

Gaisuwa mai tarin yawa da ˚auna a kodayaushe. Yaya karatu? Ina fata dai ka fi ni

bayar da himma wajen karatu.

Bayan haka, na ga wasi˚ar da ka rubuto mini, kuma na yi farin ciki matu˚a, domin

na jima ban ji daga gare ka ba. Idan Allah ya so, da an yi mana hutu zan zo gidanku.

Batun sabuwar motar babana kuwa, na samu labari daga wajen yayana. Kwana shida

da sayan motar ya sanar da ni ta wasika. Idan mun zo hutu zan ce Baba ya ∂auke mu

a cikinta mu zaga gari, mu yi ∂ani, Na gode, Allah ya bar zumunci.

Ni ne abokinka har abada,

Hassan

Hausa Pry 4.indd 13 9/11/14 8:45 AM

Page 20: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

14

Ga wata wasi˚a da Idi da ke zaune a gida mai lamba biyar,layin Kimawa a jihar Kano,

ya rubuta wa yayansa Audu, da ke zaune a Legas.

Gida mai lamba 5,

Layin Kimawa,

Akwatin Gidan Waya 678, Wa˚afi

Kano,

Jihar Kano. Aya

8 ga Afrilu, 2010.

Zuwa ga Yaya Audu,

Gaisuwa mai ∂imbin yawa da so da yarda da girmamawa. Yaya aiki? Ina fata

dai kuna nan lafiya kai da iyalanka. Bayan haka, na rubuto maka wannan wasi˚a ne,

saboda ‘yar damuwar da muka shiga ganin ba ka zo bikin abokinka Musa ba. Kowa

yana ta tambaya, Allah ya sa dai komai lafiya?Don haka na ga ya dace na rubuto maka

domin mu ji wane irin hali kake ciki. Baba da Mama da sauran mutanen gida, duk sun

ce a isar masu da gaisuwarsu. Bissalam, ka huta lafiya.

Daga ˚aninka,

Idi Auta. Aya

Aiki

arasa rubuta wannan wasi˚a da ke biye, ta hanyar cike gurabun da aka bari da

kalmomin da ke ˚asa.

Hausa Pry 4.indd 14 9/11/14 8:45 AM

Page 21: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

15

Gida Mai…………25,

Layin Mai Kwanoni,

.…… gidan waya 998,

Kaduna,

Jihar Kaduna.

4………Janairu, 1990.

Zuwa ga…………,

Bayan……………da…………alheri. Na rubuto wannan ………ne domin in tambayi

lafiyarka. Bayan……., ina mai sanar da kai cewa saura sati biyu mu yi bikin ………

karatun Al’˚ur’ani. Ina fatan idan da hali, za ka sami damar halarta. Ina so kuma na isar

da gaisuwata ga kawunka Malam Mudi. Wasalam ka…………. lafiya.

Ni ne abokinka,

Matin Yalwa.

Kalmomi

1. Haka

2. Ga

3. Wasi˚a

4. Huta

5. Lamba

6. Fatan

7. Gaisuwa

8. Akwatin

9. Saukar

10. Abokina

Tambayoyi

1. Mece ce wasi˚a?

2. Shin ka/kin ta∫a rubuta wasi˚a?

3. Kawo biyu daga cikin muhimmancin wasi˚a.

Hausa Pry 4.indd 15 9/11/14 8:45 AM

Page 22: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

16

4. Mene ne yake fara zuwa a farkon wasi˚a?

5. Da me ake rufe wasi˚a?

6. Adireshi nawa ake da su a irin wannan wasi˚a.

7. Idan January shi ne Janairu a Hausa, to February shi ne __________ .

a) Febuwari b) Faburairu c) Febuari d) Feburuare

8. Akan rubuta wasi˚a, don aikawa da __________ .

a) mutane b) magana c) sa˚o

9. Bayan gabatarwa sai kammalawa a rubutu wasi˚a.

a) Ee b) A’a

10. Adireshin mai rubuta wasi˚a ne kan zo a farkon wasi˚a.

a) Ee b) A’a

Aiki

1. Rubuta wasika zuwa ga yayanka, kana neman ya kawo maka ziyara makaranta.

2. Rubuta wa ˚awarka wasika kina mai gaya mata cewa za ki kawo mata ziyara

idan an yi hutun makaranta.

3. Rubuta wasika zuwa mahaifinka, kana mai shaida masa cewa ka samu

kyakkyawan sakamo a jarrabawar da kuka yi.

4. Rubuta wasi˚a zuwa ga mahaifiyarki, kina sanar da ita cewa kun fara jarrabawa.

Jagora

Yana da kyau malami ya ˚ara kawo wa ∂alibai, samfurin wasu wasi˚u iri daban-daban

don su ˚ara fahimtar darasin sosai. Haka kuma malami ya ba wa ∂alibai, aikin rubuta

wasi˚a gajeriya. Yara su rubuta akalla ∂aya daga wasikun da ke cikin aiki.

Hausa Pry 4.indd 16 9/11/14 8:45 AM

Page 23: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

17

Babi na 7

Fara koyon ka’idojin rubutu

Manyan ba˚a˚e

B ı C D Î

F G H J K

L M N R

S T W Y Z

ananan ba˚a˚e

b ∫ c d ∂

f g h j k

˚ l m n r

s t w y z

Manyan da ˚ananan wasula

A I O U E

a i o u e

Aiki

Samar da ˚ananan ba˚a˚e, ta manyan guraben da aka bari.

Hausa Pry 4.indd 17 9/11/14 8:45 AM

Page 24: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

18

B b _____ ∫ _____ ∂

F _____ _____ g _____ h

_____ M _____ _____ n

_____ r T ______ _____ w

_____ a _____ e L ______

_____ s _____ y Z ______

______ u ______ i ______ j

______ k C ______ _______ o

D ______ _____˚y ______ gw

Wuraren da ake amfani da manyan ba˚a˚e

Akwai wurare da dama da ya zama wajibi a fara rubuta su da manyan ba˚a˚e a

yayin da ake rubutu. Wa∂annan wurare suna da matu˚ar muhimmanci.

Muhimman wuraren da ake fara rubutawa da manyan ba˚a˚e su ne kamar haka:

1. Farkon magana: Ana amfani da babban ba˚i a duk farkon magana. Dole ne a

fara yin amfani da babban ba˚i a duk inda aka ∂iga aya, kuma za a ci gaba da

rubutu. Misali:

a) A wani gari an yi wani babban malami mai suna Jafaru. Babbar sana’arsa

ita ce noma.

b) Samir yana da ˚o˚ari a makaranta. Ba ya wasa da karatunsa ko ka∂an.

2. Sunan littafi: Sunan da aka ambaci littafi ana fara rubuta shi da babban ba˚i.

Misali: Magana Jari Ce, Bala da Babiya, Wasan Marafa, Iliya Îan Mai ˚arfi da

sauransu.

Hausa Pry 4.indd 18 9/11/14 8:45 AM

Page 25: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

19

3. Bayan alamar tambaya: Ana tashi da babban ba˚i bayan alamar tambaya.

Misali:

a) Hasan ka ci abinci? Hasana ta ci nata.

b) Audu ne ya tafi ? Hassan ne ba Audu ba.

4. A farkon saki-layi: Ana tashi da babban ba˚i a farkon sakin-layi, Misali:

Makarantar su Samir tana da girma sosai. Akwai manya-manyan bishiyoyi masu

tarin ganyaye, da suke samar da iska mai da∂in gaske da shiga jiki. Îalibai suna

jin da∂in yin wasa a filin makarantar.

Wata rana aka shirya gasa a tsakanin makarantar su Samir da ‘yan makarantar

Filin wallo da ke ma˚wbtaka da su.‘Yan makarantar su Samir ne suka lashe

wannan gasa.

5. Sunan ubangiji: Ana fara rubuta sunan Ubangiji da babban ba˚i. Misali:

Allahu, Arrahamanu, da sauransu.

6. Sunayen Annabawa : Ana fara rubuta sunayen annabawa da manyan ba˚a˚e.

Misali: Annabi Muhammadu (SAW), Annabi Musa da sauransu.

7. Sunayen mala’iku : Ana fara rubuta sunayen Mala’iku da manyan ba˚a˚e.

Misali:

Jibrilu, Mika’ilu, Rilwanu da sauransu.

8. Sunayen mutane: Ana fara rubuta sunayen mutane da babban ba˚i. Misali:

Binta, Adamu, Maryam da sauransu.

9. Sunayen ˚asashe da garuruwa da unguwanni: Ana fara rubuta sunayen

˚asashe da garuruwa da unguwanni da babban ba˚i. Misali: Nijeriya, Kamaru,

Amurka, Kano, Zariya, Yakasai, Goran-dutse da sauransu.

11. Sunayen kofofin gari da kasuwanni da tsaunuka: Ana fara rubuta dukkan

wa∂annan da babban ba˚i. Misali: Kofar kabuga, Kofar sauri, Sabon-gari,

Kantin Kwari, Dutsen-Dala, Dutsen-Arfa da sauransu.

12. Sunayen koguna : Ana fara rubuta sunayensu da babban ba˚i. Misali: Maliya,

Nilu da sauransu.

13. Sunayen watanni da ranaku: Ana fara rubuta su da manyan ba˚a˚e.misali:

Janairu, Mayu, Faburairu, Litinin, Laraba da sauransu.

14. Sunayen kabilu da harsuna da addinai: Ana fararubuta wa∂annan da

manyan ba˚a˚e. Misali: Hausawa, Larabawa, Turanci, Indiyanci, Musulunci,

Kiristanci da Sauransu.

Hausa Pry 4.indd 19 9/11/14 8:45 AM

Page 26: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

20

15. Kamfanoni da ˚ungiyoyi : Ana fara rubuta su da manyan ba˚a˚e. Misali:

Ma∂aba’ar NNPC, ungiyar tsofaffin ∂alibai, Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da

sauransu.

Aiki

Gyara wannan rubutu ta hanyar sanya manya da ˚ananan ba˚a˚e a wuraren da suka

dace.

A cikin littafin iliya ∂an mai ̊ ari an bayya sunan allah da annabawa da malaiku kamar

jibrilu da mika’lu da kuma sunayen matane kamar; binta da adamu da samons. Akwai

kuma sunaye kamar kano da nijeriya da gusau da litinin da asabar da sauransu.

Hausa babbar ˚abila ce Nijeriya. jigawa da anambra da abia duk garuruwa ne nijeriya.

Akwai makarantu kamar abu da buk da sauransu.

Wuraren da ake tashi da karamin ba˚i

1. Bayan wa˚afi: (,)

Ya sha ruwa, ya ci gaba da aiki, sannan ya tafi.

2. Bayan wa˚afi mai ruwa(;)

Audu ya tashi, ya tafi makaranta; da aka tashi ya dawo.

3. Yayin da ake rubutu ba a ˚are ba:

Samir da Hassan abokai ne, tun suna yara.

4. Wajen lissafa abubuwa:

Kasuwa da gida da asibiti duk gine-gine ne.

Tambayoyi

1. Kawo wurare uku da ake amfani da babban ba˚i.

2. Da wane irin ba˚i ake fara rubuta sunayen garuruwa?

3. Mayar da wa∂annan ˚ananan ba˚a˚e zuwa manya;

a) ∂

b) ˚

c) ∫

4. Kawo wurare guda biyu da ake rubutawa da ˚ananan harufa.

5. Shin bin ˚a’idojin rubutu suna inganta rubutu?

6. Ba˚in da ke nuna ˚aramin ba˚i na ‘B’ shi ne ___________ .

a) ∂ b) ‘b c) ∂’ d) d

Hausa Pry 4.indd 20 9/11/14 8:45 AM

Page 27: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

21

7. Wasalin ‘a’ yana komawa __________ a babban ba˚i.

a) H b) A c) R d) a

8. Ana rubuta sunan littafi ne da ˚aramin ba˚i.

a) Ee b) A’a

9. Sunayen annabawa da mala’iku ana rubutasu da babban baki

a) Ee b) A’a

10. Dukkan wa∂annan ana rubuta su da babban ba˚i a tsakiyar rubutu banda

∂aya.

a) Adamu b) Maryam c) Garba d) Ruwa

Aiki

Wannan rubutu da ke biye ba ya bisa ˚a’idar rubutun Hausa, domin an cire wasu

alamomin rubutu irin su aya da wa˚afi da alamar tambaya. Sannan an cire manyan

ba˚ake a wuraren da suke.

Umarni: Sake rubuta wannan rubutu tare da sanya shi cikin ˚a’ida.

kafin in shiga gida guda ya tarad da ni ya yi wuf ya cafe mini wuya ya ce ina zoben

da na ∂auka a masallaci yanzu na yi nan tarai-tarai na yi nan tarai-tarai duk Gabana

na fa∂uwa na ce wallahi ban ∂auki zoben ba. suka ce ˚arya nake yi na ∂auka

Jagora

Malami ya ba wa ∂alibai wasu jimloli, da ba su da ˚a’idojin rubutu domin su daidaita

˚a’idojin rubutunsu. Malami ya jagoranci ∂alibai, wajen ˚ara tantance manya da

˚ananan harufa. Yadda ya kamata a rubuta wannan rubutu yana ˚arshen littafin.

Malami ya yi amfani da shi don yi wa yara gyara.

Hausa Pry 4.indd 21 9/11/14 8:45 AM

Page 28: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

22

Babi na 8

Gajerun wasannin kwaikwayo

Wasan kwaikwayo kamar yadda sunansa ya nuna, wasa ne da ake gina shi don

kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwa, da ake son isarwa ga jama’a.

Wasan kwaikwayo na Hausa ya kasu zuwa gida-gida kamar haka:

1. Wasan kwaikwayo cikin tashe.

2. Wasan kwaikwayo rubutacce.

3. Wasan kwaikwayo na dandali.

4. Wasan kwaikwayo na rediyo.

5. Wasan kwaikwayo na talabijin.

6. Wasan kwaikwayo na fim.

7. Wasan kwaikwayo na sinima.

Wasan kwaikwayo cikin tashe

Tashe wata al’ada ce ta Hausawa wadda ta samu bayan zuwan Musulunci, wadda

yara (maza da mata), da manyan maza suke aiwatar da ita a yayin da watan Ramalana

ya kai kwana goma. Wasu daga cikin wasannin kwaikwayo cikin tashe sun ha∂a da;

Na maza

Tsoho da gemu

A wajen aiwatar da wannan wasa na tashe, yara suna kwaikwayar shigar tsofaffi,

ta hanyar sanya farin gemu da saje ta yin amfani da auduga, sannan wanda ya yi

wannan shiga, zai dinga nuna gajiyawa irin ta tsofaffi, ta hanyar takwarkwashewa da

nuna rashin ˚wari, su kuma ragowar yara suna tallafar sa. Ana yin wa˚a yayin aiwatar

Hausa Pry 4.indd 22 9/11/14 8:45 AM

Page 29: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

23

da wannan tashe. Wannan wa˚a ta ˚unshi fa∂akarwa, a kan sanya tausayi a zukatan

yara, da kuma tallafar mutumin da ya tsufa ko ˚arfinsa ya ˚are.

Tsoho da gemu,

Amshi: Ya tsufa.

A tallabe shi,

Amshi: Ya tsufa.

A ba shi na Allah,

Amshi: Ya tsufa.

A taimake shi da dawa,

Amshi: Ya tsufa.

A agaza masa,

Amshi: Ya tsufa.

Na mata

Ragadada

A wannan wasa, yara mata kamar shida ne suke ha∂uwa, sai ∂aya daga cikinsu ta

sa kaya yagaggu, kuma masu dau∂a domin nuna rashin isasshiyar sutura, saboda

saye-sayen da ba su dace ba na kwa∂ayi. Ragowar matan kuma na biye da ita, suna

amsa mata wa˚ar kamar haka:

Hausa Pry 4.indd 23 9/11/14 8:45 AM

Page 30: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

24

Ragadada

Amshi: Ta hana ki riga.

Îanwake,

Amshi: Ya hana ki zani,

Shasshaka,

Amshi: Ta hana ki ∂ankwali.

Soye ma,

Amshi: Ya hana ki takalmi.

Ragadada,

Amshi: Ta hana ki riga.

Wasan yana fa∂akarwa a kan wasu munanan halaye, kamar ˚walama da

kwa∂ayi. Haka kuma, wasan yana fa∂akarwa a kan kishin zuci, da neman abin kai, da

tattali, da adana shi. Har wa yau, wasan yana fa∂akarwa kan saye-sayen da ba shi da

amfani, wa∂anda daga ˚arshe, ko suturar kirki mutum sai ya rasa.

Tambayoyi

1. Kawo ire-iren wasan kwaikwayo guda uku.

2. Me ake kwaikwaya a wasan kwaikwayo?

3. Yara kamar guda nawa ne suke aiwatar da wasan ragadada?

4. Kawo abubuwa guda uku, da ake amfani da shi a wasan tsoho da gemu.

5. Shin wasan kwaikwayo yana fa∂akarwa?

6. Yaushe ake aiwatar da wasan kwaikwayo cikin tashe.

a) A lokacin watan sallah b) Da bikin mauludi

c) A lokacin da watan Ramalana ya kai goma.

7. Wasan tsoho da gemu, wasa ne na maza?

a) A’a b) Ee c) Wasa ne na mata

8. Wasan kwaikwayo, wasa ne da ake gina shi, don kwaikwayon wani labari ko

wata matsala ta rayiwa.

a) Ee, ana gina shi don kwaikwayon wata matsala ta rayuwa.

b) A’a don bukukuwan al’ada. c) Don nuna wasanni.

Hausa Pry 4.indd 24 9/11/14 8:45 AM

Page 31: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

25

9. Tashe ana aiwatar da shi ne ___________ .

a) Bayan zuwan musulunci b) Bayan zuwan Larabawa

c) Kafin zuwan Turawa da Larabawa

10. Wane darasi wasan ragadada, wanda mata suke yi yake koyarwa?

a) Kishin zuci da neman abin kai da tattali.

b) Shashanci. c) Son abin duniya.

Jagora

Malami ya kawo wasu wasannin kwaikwayo gajeru, daga littafi, don karantawa

tare da ∂alibai. Malami ya shirya wa ∂alibai gajerun wasan kwaikwayo, domin

su aiwatar a aji.

Hausa Pry 4.indd 25 9/11/14 8:45 AM

Page 32: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

26

Gajerun wakoki

Wa˚ar bin iyaye

Da sunan Ta’ala Ilahi na fara,

Bisa wanga tsari da zan rattaba.

Ina yin salati ga Manzo fiyayye,

Har zuriya Alihi Sahaba.

Na yi nufin zan yi wo garga∂i,

Wurin masu raina uwa da uba.

Abin da wa∂ansu suke wa iyaye,

Ko da kare yanzu ba zai ci ba.

Sun ∂au iyayensu tamkar barori,

Ko kafiri bai yi wo haka ba.

Uba zai wuce ga shi ∂auke da kaya,

Ga ∂ansa ba za ya kar∫e shi ba.

Sukan kama sunan iyaye a fili,

Tamkar abokinsu ba fargaba.

Babi na 9

Hausa Pry 4.indd 26 9/11/14 8:45 AM

Page 33: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

27

Sunan uwa zahiri za su kama,

Ba za su ∫oye su ce Iya ba.

Don ma wula˚anta girman iyaye,

Su karkata hula su je gun uba.

Mata ko sun karkace fatala,

Sunanta wai, ‘Baba-ban-gan-ka-ba’.

Ko gaisuwa yanzu ta gagara,

Ba za su gai da uwa da uba.

Akwai masu zagin iyaye suna nan,

Tamkar uwa ba ta haife su ba.

Zagin iyaye yana sa bala’i,

Da cuta da ba za ta sawwa˚a ba.

Allah wadan masu zagin iyaye,

Ko sun yi ro˚o ba a ba su ba.

Ibadarsu ko ta ciko duniya,

Ku tabbata Allah ba zai yarda ba.

A nan duniya ba shi yin arziki,

A can Lahira kuma ba marhaba.

A nan duniya babu haske gareshi,

A can lahira kuma ga fargaba.

Hausa Pry 4.indd 27 9/11/14 8:45 AM

Page 34: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

28

Muhimman kalmomi

Kalma Ma’ana

1. Rattaba Tana nufin rubuta

2. Zuriya Tana nufin dangi

3. Sahaba Tana nufin Sahabbai

4. Barori Ana nufin masu hidima da aikace-aikace

5. Zahiri Tana nufin a fili

6. Fatala Nau’in ∂ankwali na mata

7. Marhaba Ana nufin sannu da zuwa

8. Haske Alheri

9. Fargaba Ana nufin tsoro

10. Baba-ban-ganka ba Wani irin ∂aurin ∂ankwali ne na rashin kunya.

11. Karkakta Tana nufin a gicciya hula ko ∂ankwali a ka, ba

kamar yadda aka saba sakawa ba

12. Fiyaye Ma∂aukali

13. Bala’i Masifu da matsaloli

14. Garga∂i Tana nufin kashedi mai zafi

15 Sauwa˚a Tana nufin samun sassauci

Aiki

Cike guraben da aka bari da wa∂annan kalmomi da ke biye:

rattaba sahaba marhaba garga∂i fargaba

baba-ban-ganka-ba Haske zuriya Fatala sauwa˚a

1. Magatakarda ya _____ hannu a kan takarda da aka aiko.

2. _____ suna ne na abin da mata suke ∂aurawa a ka.

3. Mata suna yin wani ∂aurin ∂ankwali da ake kira__________ .

4. Îa mai biyayya, iyaye suna yin ________ da shi.

5. Masu raina iyaye, dole ne a yi musu ______ don gudun fa∂awa halaka.

6. Ina yin salati ga Manzo fiyayye, har zuriya Alihi sahaba don samun_______ .

7. Masu ˚in bin iyaye, sun zama abin __________ .

Hausa Pry 4.indd 28 9/11/14 8:45 AM

Page 35: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

29

8. ________ na ˚yamar masu rashin bin iyaye.

9. ________ sun bi Manzo, su kuma yi bi yayaga iyaye.

10. Yana da kyau malami ya ________∂alibai a wajen koyarwa.

Tambayoyi

1. Me wannan wa˚a take koyarwa?

2. Shin yana da kyau ˚in bin iyaye?

3. Mene ne sakamakon me raina iyayensa?

4. Za a amsa addu’ar mai sa∫awa iyayensa?

5. Me wa∂annan kalmomi suke nufi a wannan wa˚a?

a) Bala’i

b) Tamkar

6. Yaya sunan wannan wa˚ar?

a) Wa˚ar bin iyaye b) Wa˚ar raina iyaye c) Wa˚ar dogaro ga iyaye

7. Fa∂i abubuwa uku da ˚in biyayya ga iyaye yake haifarwa.

8. Biyaya ga iyaye abu ne mai muhimmanci a rayuwa.

a) A’a b) E e haka ne

9. Yaya sunan ∂aurin da mata suke yi a kansu har su karkata fatala.

a) Baba-ban-ganka ba b) Baba-ina-zuwa c) Baba-kalli-˚eya-ta

10. Barori na nufin__________ .

a) Almajirai b) ‘Yammata c) Masu hidima da aikace-aikace

d) ‘Ya’yan gidan sarki

Jagora

Malami ya jagoranci ∂alibai, wajen karanta wannan wa˚a ta hanyar rera ta, sannan

ya kawo wasu wa˚o˚in daga littattafai, domin su rera su tare da ∂alibai. Haka nan,

malami ya sa ∂alibai su fito da muhimman kalmomi.

Hausa Pry 4.indd 29 9/11/14 8:45 AM

Page 36: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

30

Babi na 10

Kacici-kaciciKacici-kacici wasa ne da yara kan ha∂u su yi, ta hanyar yi wa junansu tamboyoyi,

wasu kuma suna bayar da amsa. Ana samun ∂aya daga cikin yara ya zama mai

tambaya, ragowar kuma su zamo masu bayar da amsa. Kacici-kacici na sanya wa

yara kaifin basira da kuma iya fahimtar maganar wa∂anda suke gaba da su.

Irin wannan wasa da yara suke yi a junansu, shi ne ya gina wannan wasa na

kacici-kacici, wanda ake yi da tunani da siffanta wasu abubuwa sanannu, ga yara

cikin wata irin Hausa mai zuzzurfar ma’ana. Ga misalan wasu kacici-kacici kamar

haka;

Hausa Pry 4.indd 30 9/11/14 8:45 AM

Page 37: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

31

Misalan kacici-kacici

Kacici-kacici Amsoshi

1. Baba na ∂aka gemu na waje Haya˚i

2. Ja ya fa∂o ja ya ∂auka Îan fulani da kayan gwanda

3. Matan gidanmu masu fararen kawuna Ta∫are

4. Iya ta zaga Baba ya zago ba su ha∂u ba Kunne

5. Ta ˚anda ba ˚ashi ba kanwa

6. Kututture uku gagara ∂auri wai

7. Akushin Baba gagara su∂i Ku∂uddufi

8. Îan baka a bayan shuri Farce

9. Daga nesa na ji muryar ˚awata Ganga

10. Gwanda lili da liyo Gwanda noma da awo

11. Na yi gida na ba ˚ofa kabari

12. Tafiya sannu-sannu kwana nesa Ra˚umi

13. Gari ya ˚one amma gidan sarki bai kone ba shuri

14. Gada mafi ˚ankanci a duniya Hanci

15. Tsinin bakin fa Ja∫a

Tambayoyi

1. Su wanene ke yin kacici-kacici?

2. Mutane nawa ne ke zama masu tambaya a wasan kacici-kacici?

3. Wane irin abubuwa wasan kacici-kacici ke sa wa yara?

4. Wace irin Hausa yara suke koya ta hanyar kacici-kacici?

5. Maganganun su wa yara suke fahimta ta hanyar kacici-kacici?

Bayyana amsoshi wa∂annan kacici-kacici.

6. Da kika kwance kai wa zai yi miki kitso?

7. Na wanke ˚warya ta, na je gabas, na je yamma, na dawo, ba ta bushe ba.

8. Îan ˚aramin falke ma ci kasuwar lahira.

9. Abu ∂il ya sauko da sauki daga kan doki.

10. Abu ∂il ya sa maigari kuka.

Hausa Pry 4.indd 31 9/11/14 8:45 AM

Page 38: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

32

Aiki

Ja layi ga dukkan amsar da take daidai kamar yadda aka nuna misali.

1. Na aiki kyakkyawar ‘yata nesa ta dawo da ciki Masara

2. Tsuma giyar kan hanya fya∂e yaro fya∂e babba Haya˚i

3. Bafulatana mai harbin bango da ∂uwawunta Toka

4. Na ga saurayi da gemu Guga

5. Burum ya ci burum Gado

6. Baba na ∂aka gemu na waje Daddawa

7. Gari na ∂aka yara na kwana da yunwa Wando

8. Bawa na kullum sai na hau shi Yunwa

9. Bakar banufa ta shiga fada Kura ta gamu da ∫arawo

10. Hanya ∂aya ta rabu gida biyu Kunama

Jagora

Malami ya kawo wasu nau’o’in kacici-kacici da ba a kawo ba a wannan babi. Malami ya

taimaka yara wajen amsa tamboyoyin da zai yi musu a cikin aji. Malami ya duba wasu

littattafai na adabi domin samun ˚arin bayani.

Hausa Pry 4.indd 32 9/11/14 8:45 AM

Page 39: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

33

Babi na 11

arin magana da maganganun azanci

Ma’anar karin magana

Karin magana zance ne ∂an ˚il, mai tattare da zunzurutun ma’ana. Abin nufi dai shi

ne jimlolin karin magana gajeru ne, wa∂anda ba kasafai kalmomin cikinsu, ke nuna

zahirin abin da suke nufi ba. Wato ke nan dai, karin magana na sakaya ma’anar abin

da ake nufi.

Misalan karin maganaAkwai karin magana, masu tarin yawa a harshen Hausa, wa∂anda ake amfani da su,

a manganganu na yau da kullum. Wasu ka∂an daga cikin wa∂annan karin magana

su ne kamar haka:

a) Mugunta fitsarin fa˚o.

b) Idan ka daka rawar wani, ka rasa turmin daka taka.

c) Da ruwan ciki akan ja na rijiya.

d) Idan fitsari banza ne, kaza ta yi mana.

e) Munafunci dodo ne, yakan ci mai shi.

f) Banza ba ta kai zomo kasuwa.

g) Allah ∂aya gari bamban.

h) Abincin wani gubar wani.

Hausa Pry 4.indd 33 9/11/14 8:45 AM

Page 40: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

34

i) A bar kaza cikin gashinta.

j) Ba a ∫ari a kwashe daidai.

k) Ba a raba hanta da jini.

l) Ciki da gaskiya, wu˚a ba ta huda shi.

m) Da ∂an gari a kan ci gari.

n) Gaba ta kai ni, gobarar titi.

o) Girman kai rawanin tsiya.

Aiki

A. Yi amfani da wa∂annan kalmomi ka/ki ˚arasa wa∂annan karin magana da ke biye.

gaskiya zanen fata mashe˚iya mage ∫ata

˚asa zai fa∂o buzu arya dami kwa∂ayi

1. ______________ fure take ba ta ‘ya’ya.

2. Zara ba ta barin __________________ .

3. Sai mun ga abin da ya ture wa ____________ na∂i.

4. addara ta riga ____________ .

5. Komai nisan jifa _______________ .

6. _______________ mabu∂in wahala.

7. ai˚ayi koma kan _______________ .

8. Ka da _______________ ba yanka ba.

9. Daga ˚in _______________ sai _______________ .

10. Hali _______________ dutse.

Hausa Pry 4.indd 34 9/11/14 8:45 AM

Page 41: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

35

B. Cike wa∂annan gurabu da ke biye da wa∂annan kalmomi da aka samar.

in ji, an ce

1. In gani a ˚as ____________ da kare ana biki a gidansu.

2. Yaya zan yi da abin da ya gagari wuta, ____________ kishiyar ˚onanniya.

3. Haka tara take ____________ma so goma.

4. Ga mu ga Allah ____________ mai dashen karmami.

5. Ba a ˚in ta mutane ____________ ∫arawo ya gudu.

6. Ashe abin ya zo____________mai tsoron wanka.

7. Nan fa ∂aya ____________ da shege ina ubanka.

8. Allah sarkin za˚i ____________ ∫arawon zuma.

9. Wari yake ____________ da makaho ga ido.

10. Allah sitiri bu˚wi ____________ kishiyar mai doro.

Maganganun azanci

Maganganun azanci wasu guntayen maganganu ne na hikima, masu kama da karin

magana. Bambancinsu da karin magana, shi ne, su ba su da ∫ari biyu. Wasu sukan

kira irin wa∂annan maganganu da salon magana, ko kuma maganganun hikima.

Misalansu su ne:

1. Jiran gawon shanu: Sa ran samun abin da babu tabbas.

2. Ihu bayan hari: Îaukar mataki bayan lokacin da ya kamata a ∂auka ya wuce.

Hausa Pry 4.indd 35 9/11/14 8:45 AM

Page 42: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

36

3. Fagar jaji: Gano illar abu, bayan illar ta riga ta faru.

4. Romon baka: Îa∂in baki Yi wa mutum zance mai da∂i, yawanci na ˚arya, don a

gamsar da shi.

5. Ruwan ido: Dawurwura wajen za∫en abu.

6. Girman kai: Nuna isa.

7. Fa∂in rai: Jiji da kai.

8. Zurfin ciki: Mutum ya ˚i fa∂ar sirrin da yake da shi.

Aiki

Cike gurabun da aka bari da kalmomin da aka samar.

ciki zagon gafiyar ˚anzon gangar

shaci tashi tona rawar sanda

1. Gyaran______________ Auzinawa.

2. Hannunka mai ______________ .

3. Labarin ______________ kurege.

4. Jifar ______________ıaidu.

5. Wa ka ci ka ______________ .

6. ______________ ˚asa.

7. Ba˚in ______________ .

8. ______________fa∂i ne.

Hausa Pry 4.indd 36 9/11/14 8:45 AM

Page 43: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

37

9. Îalibai sun yi ______________ gani.

10. Ya ______________ masa asiri.

Jagora

Malam ya kawo wasu nau’oin. maganganun azanci; tare da neman ∂alibai su fa∂i

ma’anoninsu.

Hausa Pry 4.indd 37 9/11/14 8:45 AM

Page 44: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

38

Babi na 12

Aure

Aure hanya ce ta zaman tare, tsakanin namiji da mace a matsayin miji da mata, bisa

amincewarsu da shaidu da kuma biyan sadaki.

Hausawa kamar sauran al’umma suna yin aure a tsakaninsu. Akwai wasu al’adu

da ake bi wajen yin aure. Wa∂annan al’adu, sun sha bamban daga wannan gari zuwa

wancan. Misali abin da ake yi a Daura ya bambanta da na Sakkwato, haka abin da ake

yi a Kano ya bambanta da na Zariya.

Aure babban al’amari ne ga ∂an’adam, domin shi ne sanadin haihuwa. Ga

Hausawa, ba a sanya wanda ba shi da aure a cikin dattawa. Saboda muhimmancin

aure, har al’ada ta yarda a yi wa maras aure ba’a ko zambo a cikin watan azumi.

Hausa Pry 4.indd 38 9/11/14 8:45 AM

Page 45: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

39

Akwai ire-iren auren a ˚asar Hausa kamar haka:

a) Auren fari

b) Auren bazawara

c) Auren sadaka

da sauransu.

Yawancin al’adun da suka shafi aure, an fi aiwatar da su ne a auren fari, wato auren

saurayi da buduruwa. Wasu daga cikin matakan da ake bi, har a kai ga yin aure a

˚asar Hausa su ne:

1. Nema: A nan da zarar saurayi ya ga buduruwa da yake so, sai ya fara neman

aurenta. Ta iya yiyuwa a ha∂u a kasuwa ko a dandali ko a wajen bukukuwan

al’ada. Saurayi yana yi wa budurwar da ya gani yana so ‘yar kyauta da ake kira,

‘toshi’. Bisa al’ada saurayi kan tura abokinsa ko wani da ya amincewa, don ya

sanar da budurwar da ya gani cewar yana sonta. Haka ita ma, idan ita ce, sai dai

ta tura ˚awarta. A wannan hali ne har iyayensu za su sami labari. Idan nema ya

yi nisa, sai iyaye su kai kayan ‘na-gani-ina-so’.

2. Baiko: Bayan an kai kayan ‘na-gani-ina-so’, sai iyayen yarinya su tuntu∫i yariyar

ko tana son yaron. Idan an tabbatar tana son sa, sai a tura wasu ‘yan’uwan

mahaifinta daga gidansu, su je su bayar da ita ga iyayen yaron.

3. Ada’a: Wannan godiya ce, da dangin saurayin da aka ba wa yarinya, su kan je su

yi a gidan su yarinyar.

4. Sa-rana: Wannan yarjejeniya ce, da ake cimma tsakanin dangin saurayi, da

buduruwa domin tsayar da ranar biki.

Biki

Biki ya ̊ unshi shagulgulan da akan taru a yi domin murnar aure. Akwai al’adu iri daban-

daban da suke gudana a wannan lokaci. Wasu daga cikin wa∂annan al’adu su ne;

1. Gudu: Gudu shi ne ziyarar da amarya da ˚awayenta kan kai gidajen ‘yan’uwa.

A ˚arshe sukan tsaya a gidan da aka shirya za a yi kamu.

Hausa Pry 4.indd 39 9/11/14 8:45 AM

Page 46: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

40

2. Kamu: Kamun amarya shi ne inda dangin amarya, da ango kan taru su tafi inda

amarya da ˚awayenta suka ∫uya. A nan ne akan samu wata tsohuwa ta shafawa

amarya lalle ko turare. Shi ke nan an kama ta.

3. Wanka: A nan ana ∂ora amarya a kan turmi, a sami wata ‘yar tsohuwa ta yi mata

wanka. A gefe guda kuma ‘yanmata suna rera wa˚o˚in wanka, don ˚arfafawa

amaryar gwiwa da habaici ga tsohuwa.

4. unshi: Wannan shi ne ˚unshin da akan taru a yi wa amarya. Danginta da na

ango ne sukan taru don yin ˚unshin. Akwai ˚unshin gidan maza da na gidan

mata.

5. Lefe: Lefe shi ne kayan aure wa∂anda suka ˚unshi tufafi, da kayan kwalliya da

sauransu. Dangin miji ne suke kai lefe gidan su amarya kafin ranar ∂aurin aure.

6. Îaurin aure: Ana sanar da ‘yan’uwa da abokan arziki. Ana tanadar sadaki da goro

da alewa domin ∂aurin aure. Bayan an taru a gidan su yarinya ko gidan waliyyinta,

liman zai nemi waliyyan amarya da ango. Daga nan sai a ˚ulla yarjejeniyar aure,

jama’a su shaida sannan a yi addu’a, a raba goro, kowa ya watse.

Hausa Pry 4.indd 40 9/11/14 8:45 AM

Page 47: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

41

7. Yinin biki: A wannan rana ne gidan su ango da amarya mata suke ha∂uwa domin

yin shagulgulan biki. Akan yi dafe-dafe da soye-soye, sannan a yi ka∂e-ka∂e da

raye-raye don nuna farin ciki. Daga nan, sai a kai amarya ∂akinta.

8. Bu∂ar kai: Wannan rana ce da amarya kan fito cikin abokan zamanta, idan tana

da su. Haka nan, a wannan rana ne iyayenta kan je su yi mata nasiha, kan yadda

za ta yi zaman aure da ha˚uri da abokan zama.

Aiki

Cike wa∂annan gurabe da kalmomin da suka dace kamar yadda ake yin bikin aure a

garinku.

1. Kayan lefe sun ha∂a da atamfa da gyale da __________,

da__________,da__________, da__________, da__________ da sauransu.

2. Gudu shi ne ziyarar da _____________________________________________

_______________________________________________________________

3. A wajen ∂aurin aure ana tanadar ________________ da ________________

da alewa ____________________ da__________,

4. Shagululan da akan taru a yi domin murnar aure, sun ha∂a da wasu

al’adu misali gudu da__________, da__________, da__________,

da__________,da__________da sauransu.

5. ‘Yammata suna rera wa˚o˚in wanka don__________,amarya

__________,da__________ ga tsohuwa.

Tambayoyi

1. Mene ne aure?

2. Kawo ire-iren aure guda biyu?

3. A ina ake yin kamun amarya?

4. A kan me ake ∂ora amarya a yi mata wanka?

5. Shin ana yin ka∂e-ka∂e a ranar yinin biki?

6. Yaushe ne ake yi wa wanda ba shi da aure ba’a ko zambo?

a) A cikin watan azumi b) A lokacin kasuwanci c) A lokacin zaman makoki

7. Wuraren ha∂uwar samari da ‘yammata, don fara neman aure sun ha∂a da:

a) A masallaci b) A kasuwa ko a dandali ko a wajen bukukuwan al’ada

c) A wajen ka∂e-ka∂e na zamani.

Hausa Pry 4.indd 41 9/11/14 8:45 AM

Page 48: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

42

8. Yarjejeniya da akan cimma a tsakanin dangin saurayi da budurwa domin tsayar

da ranar biki ita ake kira ______________ .

a) baiko b) sa-rana c) nema

9. Hausawa ba sa sanya wanda ba shi da aure a cikin jerin dattawa.

a) A’a b) Ee

10. Akan yi dafe-dafe da soye-soye da ka∂e-ka∂e da raye-raye don nuna farin ciki

musamman ranar_______________ .

Jagora

Malami ya ̊ ara fito wa da ∂alibai, irin muhimmancin da yake tattare da aure. Malami

ya yi wa ∂alibai ˚arin bayani, game da matakan yin aure, da irin bambancin da ake

samu tsakanin garuruwan ˚asar Hausa.

Hausa Pry 4.indd 42 9/11/14 8:45 AM

Page 49: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

43

Babi na 13

Hausawa da sana’o’insu

Ma’anar sana’a

Sana’a wata aba ce da mutum yake yi, domin samun abin masarufi, wajen gudanar da

harkokin rayuwa na yau da kullum. Haka kuma sana’a ta shafi sha’anin kasuwanci,wato

harka ce ta saye da sayarwa. Sannan sana’a hanya ce ta sarrafa albarkatun ˚asa,

kamar su amfanin gona da dabbobi da tsirrai da sauransu. Hausawa suna da

sana’o’insu na gargajiya masu tarin yawa, wa∂anda suka gada tun iyaye da kakanni.

Ire-iren sana’o’in Hausawa, sun ha∂a da sana’ar noma da fawa da ˚ira da wanzanci

da jima da su da sassa˚a da dukanci da sa˚a da rini da sauransu.

Bayanin wasu sana’o’in Hausawa

1. Noma: Noma ita ce babbar sana’ar Hausawa, kuma mafi muhimmanci. Sana’ar

noma, sana’a ce ta tona ˚asa da fitar da amfaninta,ta hanyar nome ta da gyara

ta da kuma yin shuke-shuke a cikinta. Noma iri biyu ne: noman damina wanda

ake yi lokacin zubar ruwan sama, sai kuma noman rani wanda ake yi da kaka

bayan ∂aukewar ruwan sama. Masu yin noma su ake kira manoma. Dangane da

kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da noma sun ha∂a da; fartanya

da lauje da magirbi da wu˚a da garma da gatari da sungumi da sauransu. Ire-iren

kayayyakin da ake nomawa su ne: auduga da gya∂a da dankali da karas da dawa

da gero da rake da masara da shinkafa da alkama da makamantansu.

Hausa Pry 4.indd 43 9/11/14 8:45 AM

Page 50: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

44

2. Jima: Jima sana’a ce da ake yi da fatar dabbobi ta hanyar cire gashi daga jikin fata,

da kuma gyara ta don samar da abubuwan amfani. Masu yin sana’ar jima su ake

kira majema. Kayayyakin da ake amfani da su a wajen sana’ar jima, sun ha∂a da:

a) Fata

b) Bagaruwa

c) Kwatanniya

d) Turmi

e) Gungume

f) Toka da ruwa

g) Kujera

h) Kartaji

da sauransu.

Akwai kuma ire-iren kayayyakin da ake samarwa daga sana’ar jima irin su;

takalmi, jaka, zabira, guru, kambu, da sauransu.

Hausa Pry 4.indd 44 9/11/14 8:45 AM

Page 51: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

45

3. ira: ira sana’a ce da ta shafi sarrafa ̊ arfe ko tama ko zinare ko azurfa ta hanyar

narkawa da wuta don samar da wasu abubuwan amfani. Masu yin sana’ar ˚ira su

ake kira ma˚era. Ma˚era sun kasu gida biyu:akwai masu amfani da ba˚in ̊ arfe da

kuma masu amfani da farin ˚arfe.

A wajen gudanar da sana’ar ˚ira, ana amfani da kayayyaki irin su:

a) ziga-zigi b) mahuji

c) uwar-ma˚era d) almakashi

e) awartaki f) gawayi

g) gudima h) wuka

Sana’ar ˚ira, na samar da abubuwa kamar haka:

a) wuka b) ∂ankunne

c) takobi d) almakashi

e) zarto f) zobba

g) sar˚a h) tukunyar karfe

i) kibiya

da sauransu.

Hausa Pry 4.indd 45 9/11/14 8:45 AM

Page 52: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

46

Muhimmancin sana’o’i

1. Samar da abin masarufi ga masu gudanar da su.

2. Samar da aiki ga wa∂anda suke aiwatar da su.

3. Bun˚asa tattalin arzi˚in masu sana’o’in da na garuruwansu.

4. Haifar da wasu sana’o’in.

5. Koya tarbiyya ga matasa masu koyon sana’o’in.

6. Samar da abinci da sauran abubuwa na musamman don bu˚atun rayuwa.

7. Cu∂anya da sauran jama’a a wuraren aiwatar da sana’o’in.

8. Samar da magunguna na musamman.

9. Kauce wa larura ta hanyar amfani da ∂an abin da ake samu daga sana’o’in.

10. Dogaro da kai da tsare mutunci.

11. Bun˚asa al’adun gargajiya.

12. Taimakon juna.

Tambayoyi

1. Wace sana’a ce ta fi muhimmanci a wajen Hausawa?

2. Kawo ire-iren sana’oin Hausawa guda uku.

3. Ambaci kayayyaki guda uku da ake nomawa.

4. Yaya sunan masu aiwatar da sana’ar ˚ira?

5. Kawo ire-iren muhimmancin sana’o’i guda uku.

Hausa Pry 4.indd 46 9/11/14 8:45 AM

Page 53: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

47

6. Wace sana’a ce ba ta gargajiyar Bahaushe ba a nan?

a) Noma b) Kira c) Walda d) Wanzanci

7. Wace sana’a ce ta saye da sayarwa?

8. Sana’ar da ake sarrafa fata ita ce______________ .

9. ______________ su suke sama wa ___________ kayan aiki.

10. Masu sana’ar jima na amfani da dukkanin wa∂annan abubuwa in ban da ______.

a) guru b) takobi c) takalmi d) jaka

Aiki

Bayyana masu sana’ar da suke samar da wa∂annan kayayyaki, ta hanyar jan layi.

Ga misali ∂aya nan an bayar.

Takalmi Noma

Fartanya Jima

Auduga ira

Takobi Noma

Guru ira

Gero Jima

Lauje Noma

Kambu Jima

Masara ira

Sar˚a Noma

Jagora

Malami yana iya duba littafin Zaman Mutum da Sana’arsa, sannan ya za∫i wasu

daga cikin muhimman kalmomi da aka ambata a cikin wa∂annan sana’o’i, don yi wa

∂alibai bayaninsu. Malami na iya shirya wa ∂alibai ziyara, zuwa wuraren aiwatar da

sana’o’in.

Hausa Pry 4.indd 47 9/11/14 8:45 AM

Page 54: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

48

Babi na 14

Abincin Hausawa

Hausawa kamar sauran al’umma na duniya, suna da nau’o’in abinci iri daba-daban.

Wa∂annan nau’o’i na abinci, sun rabu zuwa gida-gida. Akwai nau’in abinci mai sa

˚oshi, akwai kuma na marmari. Akwai kuma abin sha wanda shi ma wasu lokutan, kan

tsaya a matsayin abinci mai sa ˚oshi. Haka kuma, akwai ganyayyaki da Hausawa kan

sarrafa a matsayin abincinsu.

Ga yadda rabe-raben abincin Hausawa yake

1. Masu sa ˚oshi da kuzari: Irin wa∂annan nau’o’in abinci sun ˚unshi:

a) Tuwon dawa ko na gero ko na shinkafa ko na masara ko na alkama da

sauransu. Ana cin tuwo da miyar kuka ko karkashi ko taushe ko ku∫ewa da

sauransu.

b) Shinkafa dafa-duka ko mai miya.

c) Alkubus da miyar taushe ko miyar agushi da sauransu.

d) Dambu da mai da yaji.

e) Îanwake da mai da yaji ko da miya.

f) Waina da miya ko da zuma ko da sukari.

g) Gurasa mai miya ko ban∂ashe.

h) Wasa-wasa

i) Dashishi

j) Burabusko

da sauransu.

2. Abincin marmari: yawancin irin wa∂annan abinci, sun ˚unshi kayan toye–toye

ne. Wa∂annan nau’o’in abinci sun ˚unshi:

Hausa Pry 4.indd 48 9/11/14 8:45 AM

Page 55: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

49

a) Nama

b) Funkaso

c) Alkaki

d) Nakiya

e) Sinasir

f) A-ci-da-mai

g) Bakilawa

h) Dubulan

i) osai

j) Fanke

k) Cincin

da sauransu.

3. Abincin da ake sha: Irin wa∂annan sun ha∂a da:

a) Kunun kanwa ko na tsamiya, ko na zaranya da sauransu.

b) Fura

c) Koko

d) Kunun za˚i

e) Farau-farau

f) So∫arodo

g) Kunun aya

da sauransu.

4. Ganyayyaki: Wa∂annan sun ˚unshi irin ganyayyakin da Hausawa kan sarrafa,

su ci ta hanyar dafawa, ko kuma su ci a haka. Misalan irin wa∂annan su ne:

a) Zogale

b) Rama

c) Yakuwa

d) Ya∂iya

e) Dinkin

f) Lamsir

g) Salak

Ganyayyaki

Hausa Pry 4.indd 49 9/11/14 8:45 AM

Page 56: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

50

da sauransu.

5. ‘Ya’yan itatuwa:

a) Mangwaro

b) Goba

c) Kanya

d) Îorawa

e) Îinya

da sauransu.

Muhimmancin abinci

Abinci yana da muhimmanci ˚warai da gaske a jikin ∂an’adam. Akwai hanyoyi

guda uku muhimmai da za a iya karkasa abinci, dangane da aikin da yake yi a jikin

∂an’adam kamar haka:

1. Abinci yana sa kuzari a jikin ∂an’adam.

2. Abinci yana gina jikin ∂an’adam.

3. Abinci yana ˚ara lafiya.

4. Abinci yana kare jiki daga kamuwa da cututtuka.

5. Abinci yana ˚ara garkuwar jiki.

Aiki

Sa layi a kan hoton abincin da ya dace da sunansa.

‘Ya’yan itatuwa

Hausa Pry 4.indd 50 9/11/14 8:45 AM

Page 57: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

51

Lemo

Gwanda

Karas

Fanke

Abarba

Mangwaro

Kankana

Ayaba

Salak

Kwakwa

Hausa Pry 4.indd 51 9/11/14 8:45 AM

Page 58: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

52

Tambayoyi

1. Kawo ire-iren abinci guda uku da kan sa kuzari?

2. Shin wasa wasa da dashishi abincin marmari ne?

3. Kawo ‘ya’yan itatuwa guda uku.

4. Kawo muhimmancin abinci guda uku.

5. Shin abinci yana kare garkuwar jiki?

6. Hausawa suna da nau’o’in abinci iri daban-daban.

a) Abinci maisa ˚oshi da na mamari da abin sha.

b) Abinci mai ∂a∂i da ruwa

c) Abinci mai sa kasala dayunwa da rama.

7. Dukkan nau’o’in abinci nan na marmari ne in ban da ______________ .

a) Funkaso b) Nama c) Burabusko d) Dubulan

8. Da me ake cin tuwo?

a) Da miyar kuka ko karkashi ko taushe ko kubewa

b) Da gya∂a c) So∫orodo

9. Abinci mai sa ˚oshi da kuzari sun ha∂a da: Shinkafa da Îanwake da

burabusko da sauransu.

a) Ee (b) A’a c) Abinci ne na mamari

10. Rashin cin abinci ga ∂an’adam, kan kawo rashin kuzani da gina jiki da ˚ara

lafiya da kare garkuwar jiki.

a) A’a b) Ee

Jagora

Malami ya sa yara su lissafo ire-iren abincin da suke ci a gidajensu. Malami ya ˚ara

fayyace wa ∂alibai, game da muhimmancin abinci ga jikin ∂an’adam.

Hausa Pry 4.indd 52 9/11/14 8:45 AM

Page 59: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

53

Babi na 15

Tufafin Hausawa

Tufafi shi ne duk wani abu da ake sa wa ko ∂aurawa a jiki, da nufin suturce al’aura da

kare jiki. Al’ummar Hausawa suna da suturunsu na yara maza da mata. Akwai kuma

na manya na maza da na mata. A cikin suturun Hausawa, akwai wa∂anda suke sa wa

yau da kullum, akwai na wani lokaci na musamman kamar sanyi da zafi, akwai kayan

da ake sa wa don yin wata sana’a, sannan akwai wa∂anda ake kira, ure adaka, wato

na ado ke nan.

1. Dangane da wannan, za a iya raba tufafin Hausawa gida biyu kamar haka;

2. Tufafin maza

3. Tufafin mata

1. Tufafin maza

Tufafin Hausawa na maza za a iya kasa su kashi uku, wato:

a) Na sa wa a kai: A nan za a samu tufafi da Hausawa suke rufe kai da su,

kamar hula da rawani. Hula wata aba ce da Hausawa suke sa wa a ka, domin

kare kansu daga zafin rana. Rawani wani ˚yalle ne, da sarakuna da malamai

suke ∂aurawa a ka.

Akwai huluna da rawani kamar haka;

Huluna Rawani

Damanga Dan kura

Zita Hirami

Dara Bakin fara

Marfiya Kuskus

Yar tofa Harsa

Hausa Pry 4.indd 53 9/11/14 8:45 AM

Page 60: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

54

Dankwara da sauransu.

Ha∫ar-kada

Zanna Bukar

da sauransu.

b) Na gangar jiki: A cikin suturun maza na Hausawa, wannan kaso su suka fi yawa. A

nan ana samun riguna marasa hannu da ̊ ananan riguna masu hannu da dogwayen

riguna da kuma babbar riga. Don haka a nan za a iya samun:

Riga ˚arama Babbar riga

‘Yar shara Sace

Jamfa Gare

‘Yar Jos Kwakwata

Doguwar riga Girken Nufe

Tazarce Wundiya

Jallabiya Aska tara

Kufta Alkyabba

da sauransu.

Wando

Hula

RigaKallabi

Hausa Pry 4.indd 54 9/11/14 8:45 AM

Page 61: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

55

c) Na sa wa a ˚afa: A nan akwai tufafin Hausawa maza da suka ha∂a da wanduna

da kuma takalma. Yawancin takalman mata ma suna iya sa wa. Wa∂annan su ne

kamar haka:

Wanduna Takalma

Tsala Fa∂e

Mai kamun ˚afa Huffi

Îan’itori Balka

Bulus Sun˚e

Îan tunis Sandal

Fanjama Kwabashu

da sauransu.

2. Tufafin mata

Tufafin mata Hausawa za a iya kallonsu ta fuskoki uku kamar haka:

Na sa wa a kai kamar:

Îankwali

Saro

Taguma

Hijabi

Mayafi

Siket Takalmi

Hausa Pry 4.indd 55 9/11/14 8:45 AM

Page 62: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

56

Na gangar jiki: Wa∂annan sun ha∂a da riguna da zannuwa. Yawancin rigunan mata

Hausawa ana yin su ne, tare da zani a ha∂e. Don haka kowane zane tare yake da

rigarsa, sai dai kawai a sami ire-ire.

Riguna Zannuwa

Riga mai hannu Bubu

Buba ∂ankatanga

Abaya Leshi

Bulawus Îantofi

Shimi Atamfa

da sauransu Sa˚i

Siket

Îan’itori

Tambayoyi

1. Mene ne tufafi?

2. Kawo ire-iren tufafin maza na sa wa a ka guda uku.

3. Kawo ire-iren zannuwan mata guda uku.

4. Su wane ne suke sanya rawani?

5. Fa∂i amfanin tufafi guda biyu.

6. Duk abin da aka sa dan suturta al’aura da kare jiki shi ne ______________ .

a) fata b) mayafi c) tufafi d) babbariga

7. Kayan da Hausawa suke adanawa, sai wani taro na musaman su ne na _____ .

a) ˚arshen kaya b) yau da kullum c) ˚ure adaka d) yin sana’a

8. Dukkan wa∂annan tufafin maza ne na sawa a kai banda ∂aya.

a) Marfiya b) Dara c) Îankwali d) Zita

9. ‘Yar shara riga ce da mata suke amfari da ita.

a) Ee b) A’a

10. Daga cikin rigunan matan Hausawa akwai tsala.

a) E e b) A’a

Hausa Pry 4.indd 56 9/11/14 8:45 AM

Page 63: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

57

AikiZabi sunan da ya yi daidai da kowane hoto.

Dara Tamfa Aska Rawani Wando

‘Yar shara Takalmi Kallabi Yar tofa

Jagora

Malami ya jagoranci ∂alibai, zuwa wuraren da ake ∂inkawa da sayar da tufafin

Hausawa, domin su gani da idanuwansu. Malami ya fito wa da ∂alibai, muhimmancin

sanya sutura.

Hausa Pry 4.indd 57 9/11/14 8:45 AM

Page 64: Hasken Karatu - api.volunteer.npvn.ngapi.volunteer.npvn.ng/media/pdfs/Hasken Pry 4.pdf · nan don ya huta. Yana zaune yana hutawa, sai barci ya fara kama shi. Can sai ya tuna da wata

58

Hausa Pry 4.indd 58 9/11/14 8:45 AM