12
Hidiman binciken aikin gona daga manufar Ikwaita Samun mafita daga dawamammen ci gaba na gida don mutane da halitta, da al’ummomi masu armashi Niger FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI GASKIYA Empowered lives. Resilient nations.

FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

Embed Size (px)

Citation preview

Page 1: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

Hidiman binciken aikin gona daga manufar Ikwaita Samun mafita daga dawamammen ci gaba na gida don mutane da halitta, da al’ummomi masu armashi

Niger

FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI GASKIYA

Empowered lives. Resilient nations.

Page 2: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

BINCIKE MASU BIYE DA JUNA DAGA MANUFAR IKWAITA (EQUATOR) DA SUKA SHAFE KUNGIYANMAJALISAN DINKIN DUNIYA MAI KULA DA CI GABAAl’ummomin gida na asali a cikin duk duniya baki daya na kokarin ci gaba don samun sabuwar dawamammen ci gaba, wanda ya daidaita da mutane da halitta. Wasu littatafai da aka baza kokuwa wani bincike da aka yi na nuna muna cikakken tarihi dangane da yadda irin wadannan manufofi ke juyawa, da iyakan tasirinsu, kokuwa wasu mutane kadan kawai suka dauki tanadin ba da wadannnan labarai, har ya kasance masanan gargajiya da Kansu ke jagoranci wannan labarai.

Wannan manufar na kungiyan ci gaba da ke karkashen Majalisan Dinkin Duniya, mai suna a turance UNDP Equator Initiative ya lura da misalai da ke nuna fasaha ko dabarun gida, da sabuwar al-adu, da jagoranci da ke cikinyadda ake tafiyad da harkankasa da dawamma: watau a turance, sustainable land management (SLM) cikin busasshen kasashe da ke cikin kasashe masu rabin hamada: (Sub-Saharan Africa) amma wannan lura ya kasance tare da kungiya mai suna ENDA Tiers Monde (ENDA), da wani kuma mai suna Open Society Initiative for Southern Africa (OSISA). Watau a Hausa jam’iyya mai manufar bude kofanta wa kowa a cikin Afrika ta kudu da al’adan mulki don hanawan kwararowar Hamada. Watau (UNCCD) wanda ya dauki nauyin wannan tarayya, shi ne Global Environment Facility (GEF) a Hausa kungiyan Duniya Mai Saukakawan damuwan muhalli. Wannan bincike mai bi nga daya ne cikin bincike da yawa; mai siffantawa ko mai ba da bayanin mafi al’ada dangane da dabarun kula da dawamammen kasa (SLM) da aka jarraba siyasan tattaunawa da ake bukarta don a samu dacewa da irin nasaran da ya daidaita saboda a kyautata matsayin ilminduniya akan muhallin gida da mafita na ci gaba; sa’annan kuma don ya kasance abin kwatance na maimaitawa ne.

Danne taswiran don ka ziyarce wurin ajiyan labarai bincike game da manufar Equator.

Masu Shirin LabarinBabban Edita (mai shirin labarin): Joseph CorcoranEdita mai tafiyad da al’amarin rubuce-rubucen: Alan PierceMasu shirin labarai da suka taimaka: Eva Gurria

Marubuta da suka taimakaAlan Pierce, Tiffany Challe, Eva Gurria, Annie Virnig, Elizabeth Shaw, Anthony von Arx, Joshua Voges, Qiang Li, Kathryn McCann

Zane-ZaneKimberly Koserowski

Godiya da amincewaEquator Initiative na ke matukar godiya a agare dukkan wadanna suka dauki hotuna da wadannan su ka yi aikin taswiran, da albarkan CIA World Facebook na duniya baki daya da Wikipedia. Muna kuma godiyan Mensah Abukari wanda ya juya rubuce-rubucen zuwa Harshen Hausa, har da Sanusi Shehu wanda ya sake bi don gyaran.

Shawara akan wadannan suka cancantu a yaba suKungiyar mai kula da ci gaban al’amarin Majalisan Dinkin Duniya, cikin shekara dubu biyu da goma sha shida. 2016. Fédération des Unions de producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series, daga New York.

Page 3: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

TAKAITAWAN TSIWURWURIFédération des Unions producteurs de Maradi Gaskiya babban kungiyan manoma ce mai manufan bincike a hanyan noma don amfanin kananan manoma na Maradi ta kasan Niger. Wannan tarayya ta kumshi hadin guwa kunguyoyi goma sha bakwai (17) da keda jimilla kananan kungiyoyin manoma dari uku da ashrin da biyar (325), da yawan mutane masu adadi dubu goma sha biyu da dari bakwai da arbain da biyu (12,742) na aiki ne don ta daukaka amfanin gonakin mambobinta, annan ta daukaka yin shiri da ya shafe kowa, da kuma ilmin kasuwancin amfanin gona da kwayoyin shuki da aka amince da su ko aka tabbatar, kamar yadda su ke bukata su sarrafa hanyoyin aikin gona. Samun manoma ya kyautata kwarai, saboda haka sun mayar wani kudi cikin albashin su asusu don dalilin ci gaban gari da jama’a baki daya. Sa’annan kuma ana kawo ma mata kwayoyin shuki mai tsiro kowane lokaci, kuma wanda ke tsiro da sauri don a dunga samun abinci kowane lokaci, kamar yadda ake bukatar a gani jarin matan karkara ya kyautata. Ana amfani da gidan rediyo na kaekara don sanarwa da ilmantarwa.

TABBATACCEN LABARAIWanda ya ci nasaran kyautan Equator cikin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu (2014)Shekaran da aka kafa kungiyan: Shekara ta dubu biyu da biyu (2002)Cibiyar kungiya: Jahar Maradi a cikin NigerMasu cin amfanin kungiyan: Hadin giwa kungiyoyi 17, Kungiyoyin manoma 325 da adadin yan kungiya 12,742Irin noma: Noman Sahel

3

JADAWALIN RUBUCE- RUBUCE

Tarihi da Muhalli 4

Babban ayyuka da sabuwar al’adu 5

Tasiri 8

Tasirin aikin gona 8

Tasirin wancan shiri akan zaman jama’a da ttatalin arziki 8

Fannin unsa 8

Tasirin siyasan 9

Dawamma 10

Maimaitawa 10

Abokanin tarayya 10

FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI GASKIYANiger

Page 4: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

44

Fédération des Unions de producteurs de Maradi Gaskiya Kokuwa a Hausa Tarayya mai Hadawan Manoman Maradi Gaskiya (mai suna FUMA Gaskiya) daya ne cikin kungiyoyin da suka fi girma cikin Afrika ta Yamma. FUMA Gaskiya na aiki cikin jahar Maradi a cikin kasan Niger. Wannan jahar Maradi na da girma ma’aunin nisa murabba dubu talatin da dari biyar, sa’annan ana ganin ta a cikin yanki da ke tsakanin kudu da tsakiya, kusan ma’aunin nisa dari shida da hamsin ta gabas babban birnin kasan, watau Niamey. Maradi na da iyaka da jahar Zinder ta gabas, sa’annan da jahar Tahoua ta yamma da kuma jahar Agadez ta arewa. Ta wajen kudu na karshe kuma, jahar Maradi na da iyaka da kasan Nigeria. Birnin Maradi ne babban birnin wannan jaha, kuma ita ne cibiyar gwamnatin wannan jaha, sa’annan ita ne birnin tattalin arzikin kasan Niger. Watau kusancin Maradi da karshen kasan Nigeria na nuna cewa akwai isasshe kasuwanci tsakaninsu.

Yawancin mazaunan jahar Maradi Hausawa ne, amma akwai wadansu kabilu tare da su har da Fulani da Baroroji da Buzaye. Galibin mazaunan jahar manoma ne ko makiyaya, tare da wadansu iyalai kadan da ke kasuwanci kokuwa aikin hannu da sana’a. Yawan gasa domin kasa dalilin sabani da tashin hankali ne tsakanin manoma da makiyayan.

Muhalli da yanayi cikin Jahar Maradi

Jahar Maradi na cikin sahel ne. Ta arewanci, akwai kananan busasshe itatuwa sosai, soboda haka ma’aunin ruwan sama bai wuce millimeter dari biyu (200) ba a cikin kowane shekara. Ta karshen kudu jahar tudu ne mai kusan kurmi, saboda haka ma’aunin ruwan sama na tsakanin millimeter dari biyar (500) da dari bakwai da hamsin (750) ne kowane shekara. Watau ana ganin wannan jahar Maradi cewa ita ce mai ba da abinci da dama cikin Niger sa’annan ta na fito da babban abincinsu da ke bukatar ruwa sa’annan ya tsiro kamar gero da dawa da wake da gweda.

Saukowan ruwa cikin kasan Afrika ta yamma mai rabin busasshen kasa ya fara bai aukuwa yadda ya kamata, da sauye-sauyen farkon damana. Tsananin ruwan sama kokuwa tsananin fari lokacin shuke – shuke suna aukuwa ne kwarai. Kasa shukar jahar Maradi na nuna galiban rashin sinadirai kasa mai kyau ko da ya ke sun rarrabu ko ina kan shimfidar wurin. Zaizayewar kasa da ragewan kurmi da yawan kiwo su ne mafarin kankantawan muhalli da ke gudanar har yau. Amma abinda ke kara batan al’amarin ne yawan mutane.

Jimlar mutanen Niger da yawan haihuwa

Watau in dai za a yi lisafin yawan haihuwan matan Niger, ana samun kowace mace na haihuwa a bakin bakwai da rabi akan matsakaitan haihuwa; wanda ya ke shi ne mafi yawan haihuwa a dunia baki daya. A yanzu in dai za a dube wancan sauyawa, yawan mutanen Niger ya karu sau biyu kafin shekara dubu biyu da talatin da daya. Jahar Maradi na daya cikin jihohi da suka fi yawan mutane sosai a Niger, kuma a yanzu yawan mutanen Niger na karuwa a a kashi uku da rabi daga cikin dari kowace shekara.

A matsakaita kasan Niger na ganin halin fari, wanda ke kawo karamcin abinci sau daya cikin shekara uku. Saurin karuwan jama’a a jahar Maradi na kara ma kasan matsuwa da ragewan amfanin gona musamman. Har yau samun amfanin gonan kwaya ya karu kadan dai ne, saboda haka ci gaban kankantawan muhalli daga sauyen yanayi zai kasance al’amari mai wuya ne idan aka dubi karshen

Hanyan mulkin wannan tarayya na FUMA Gaskiya

FUMA Gaskiya na da tarayyan manoman gona sha bakwai da kungiyoyin manoma masu adadi dari uku da ashrin da biyar da yawan mutane masu adadi dubu goma sha biyu da dari bakwai da arbain da biyu. Mai mulkin FUMA Gaskiya ne babban majalisa, wanda a cikin ta akwai wakilai uku daga kowace tarayyan manoma. Cikin farkon alhakin babban majalisan ne shiryawa da amincewa da ayyuka masu gajeren lokaci da matsakaicin lokaci da tsawon lokaci, tare da zanen shawarwarin matsayai da dokokin cikin da kuma gyaran dokokin daga baya har da amincewa da kasafin kudin kungiyan da zabe da duban aikin mashawarta. (cikin majalisan mashawarta, akwai yan kungiya bakwai daga kungiyan manoma) Akwai kuma kwamitin duba (mai tare da mutane uku). Babban majalisan na gamuwa sau biyu cikin kowace shekara. Majalisan mashawartan na karkashin babban majalisan ne kuma ita ke gudanar da ayyuka da yanken shawara da babban majalisan ta ba ta iznin yi, har da shirin tarurruka, da aiwatarwa ayyuka, da sanarwa na dabarun ci gaba da nadawan mai gudanarwan majalisan, da tabbatarwa da aikin ma’aikata da kuma wakiltawan FUMA Gaskiya a kotu a kowane hali. Mashawartan na da izini su kafa kwamitocin na musamman domin su aiwatar ayyukan kungiyan (misali sayayyan iri kokuwa taki da kwamitin gudanar da aikin makarantu).

Tarihi da Muhalli

Page 5: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

5

Babban ayyuka da subuwar al’adu

Manufofin FUMA Gaskiya sune ne domin ta taimaka zuwa ci gaban kungiyoyin manoma masu zama a yankunan karkaran na yankin Maradi saboda tattalin arziki da zaman jama’a da al’ada da fasaha. Kungiyar na cika manufofin ne bayan ta kai ma yan kungiyan sabuwar ilmin noma wanda zai kawo karuwan abinci da wadata da karuwan armashi.

Gabartawa da dawamammen aikin gona

Duk de canzan yanayi da rashin samun ruwan sama, da zayzayewa kasa, da regewan amfanin gona da dogon fari, manoman yankin Maradi sun ba amsan wancan damuwa ta hanyar canzawan hanyoyin noma saboda su kyautata halin muhalli da jama’a baki daya. FUMA Gaskiya na taimakawa domin inganta ayyukan ta hanyoyi dabam dabam misali ta na sayen taki da iri na gari da kwaya mai yawa don yan kungiyan saboda su tabbatar cewa sun dace da samun su a lokacin da ya kamata kuma ba da tsada ba. Sabuwar al’adan rabawan kaya ko

ina cikin kasa, har da kanti mai tafiya, da kwayoyi na shuka, da kasuwa na musamman mai nuna kwayoyi dabam dabam na iya sa hanyoyin rabawan kwayoyin na kauyuka ya dawamma, sa’annan kuma ya na saukaka kutsawan kasuwanci cikin yankuna masu nisa. Kintsawan kwayoyin shuka cikin kananan buhu na sa kudin kwayoyin ya saukaka, alhalin ya na rege batarwansa. (Tsakanin 2010 da 2012, FUMA Gaskiya ta sayar da kwayoyi da ke cikin kananan buhu mai adadi dubu talatin (30,000) cikin kauyuka dari da sabain 170).

FUMA Gaskiya na mayar da hankali akan watsawa dabarun noma mai sauki da ke dogara akan albarkatun gida wanda akwai ne, saboda galibin yan kungiyan mazaunan yankunan karkara da masu guzuri ne. A na ilmanta da manoma domin su yi amfani da tokan itace da taki na gida maimakon takin bature mai tsada. Ana kuma tarbiyyatar da su don su fara noman gonakin su da wuri, da kuma yin amfani da sabuwar dabaru na dasawa domin su daukaka darajar kwayoyin kasa da karuwan saurin tsirowan kwayan shuka. Gero babban abincin Niger ne amma bai tsira a yawan lokaci saboda rashin ruwan sama kokuwa barnan kwari da tsuntsaye da beraye. Yin amfani da ilmi da zai kare dashe, sabuwar ilimi ne mai manufan ya kara tsiran dashe. Ana ilmanta da manoma yadda ake jujjuya kwayan gero da gaurayan yumbu, yashi da kashin dabbobi da rubebbe abubuwa, da gawayi, da taki, da tokan itace, da ruwa don su girka karamin da’ira. Bayan haka sai a busad da’iran nan take domin a hana tsiran kwayan. Bayan an shuka wannan da’ira mai tsaba ko kwayan, ya na rike danshi da ke cikin da’ira ne alhalin ya na sake ko ya na ba da dashen abin gina jiki. Aiwatarwa wannan dabara na da’iran kwaya ya daukaka kuzarin abin shuka da amfanin gona sa’annan ya na rage rashin girman amfanin gona.

FUMA Gaskiya ta gabatar da shukan kwayoyin da amfanin gona da ke kara kyawon halin yanayi kwarai, misali dassayen tsiro tsakanin tsiro, da hadawan tsiro da itatuwa, da hadawan tsiro da itatuwa da dabbobi. Wannan hanya na kara ni’iman kasa da tsarin kasa da sake zagayowar sinadarin gina jiki. Shuke – shuken amfanin gona dabam dabam na ba da manoma tsaron arzikin kudi da abinci da armashi domin kasadan aikin ya bazu. Dangane da aikin gona da aka bude fadin sa ta hanyan

Page 6: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

6

shuke – shuke iri dabam dabam, dukka wadannan manoma na da babban tsari game da fari da damuwan kwari, watau in guda ya kasa yi, duk da haka gonan ya kawo abinci da kudi. FUMA Gaskiya na karfafawa yan kungiyan ta su yi amfani da shuke – shuke iri dabam dabam ta hanyan zaba da riken shuke – shuke iri dabam dabam na gida.

Hadin kai wurin binciken cikin gona

Hadin kai wurin bincike ya kawo ma FUMA Gaskiya wadansu cikin sakamakon su da su ke mafi kyau. Wadannan hadin gwiwar da ya shafe manoma da masanan kimiyya na da tushen ta cikin yin shawarar da ke tare da hadin gwiwar ne, kuma wadannan hadin gwiwar sun dogara akan girmamawa juna da kaunan sabobin ra’ayoyi ne. Manoma ke da alhakin noma da kimantawan shuke – shuke. An gano kan jarabawa da a ke yi cikin gona, halayan shuka da ya daidaita da na gida, wanda a ke zaben don a kara jarabawa da yaduwa. (Misali, lokacin da shuka ke yin fure ko kuwa shuka ya yi rayuwa duk da barnan kwari). A cikin tsarin binciken hadin gwiwar, manoma da kansu na iya yanke shawara akan shuka da suka fi so, sa’annan kuma irin hanyan sarrafawa da su ka fi so. Wannan na karfafa fadin cewa sakamakon bincikin daga wurinsu ya fito. Akan haka wannan hanyan hadin gwiwar zai tabbatar cewa ganin daman zaben na tafiya ko kuwa ya daidaita da bukatan manoman musanmman.

Hidiman Bincike mai suna – THE CORE WA

Cikin wannan hidiman bincike da ma’aikatar kasan Jamus da ke kula da tattalin arziki da gamayya da ci gaba ya dauki nauyin gudanar da shin, FUMA Gaskiya ta shiga cikin binciken hadin gwiwar na kungiyoyin manoman kasashe na yankunan dabam dabam da ya shafe musamman kasashen Mali da Burkina Faso da Ghana. Sa’annan manufan binciken ne don ayi kwankwanton ganowa yadda manoma ke daidaita da yawan sauye sauyen yanayi daga arewacin Sahel zuwa sashin arewacen kasar Guinea, inda sauyin yanayin ya fi yawa. Kungiyan manoman FUMA Gaskiya da ke cikin Serkin Hausa : watau

wani yankuni da adadin ruwan saman ta na da a kaddarance ma’auni millimeter dari hudu (400) zuwa dari biyar (500) ya kasance ya na daya cikin wajajen binciken da su ke mafi karshen arewa.

Daga cikin manufofin hidiman ne don a samu gero da ke mafi kyau, mai kayyaddade hali da manoman suka fi so; wanda za a iya yin amfani da shi a wajaje da yawa, masu yanayi dabam dabam cikin jahar. Manoman serkin Hausa sun aiwatar wannan jarabawa da a ke yi cikin gona a take akan wadansu shuka da ke rayuwa duk da yanayin, sa’annan su ka zabe shuka da su ka fi so lokacin kaka, inda maza da mata, kowanne ke wuri dabam dabam don kimantawa don su gane shuka da ya fi daraja, sa’annan su ka nuna gero da a ka girba gaban kowane fili na bincike don su kimanta su; sai su ka tura kati da aka shafa wa fenti masu launi dabam dabam (algashi danyen na nuna “Kyau” sa’annan rawaye na nuna “matsakaici” sa’annan “ja” na nuna kyau) cikin ambulo. Wannan hanya ya bar manoman da masu ilmin bincike sun gane irin so da tsakanin taron mata da maza kowanne ya fi so cikin filayen.

Maza da mata tare sun nuna son shukan gero da ke da dogon zanko domin saukin hadawan su baki daya in za a daure don tafiya da su cikin abin sufuri. Amma matan kuma sun gano ma wadansu shuke – shuke masu garkuwa, da zanko da su ka fi so domin binciken daga baya da jarrabawan shuka. Wannan so ya rarrabu biyu ne, farko, ya dace da na gida domin yin furen shi da wuri, sa’annan na biyu zanko nan na hana tsuntsaye da kwari da ke cin kwayoyin su yi barna. An dace sosai da jarrabawa da su ka biyo, sai kuma yanzu ana samun kwayoyin domin dayawan su wajaje masu yawa cikin kasar Niger. Manoma sun kuma zabe Karin shuke – shuke domin Karin binciken daga baya da jarrabawa da ke dogara akan halayen shuke – shuke kamar tsayayya wa wannan muguwar ciyawa gaugaai ko kudiji (Striga spp.) da tsayayya wa hunhuna da darajar sinadirai.

Daga Abokin Tarayyan Bincike har zuwa Shugaban Bincike

FUMA Gaskiya ta fara daga zaman abokin tarayyan bincike har ta kasance shugaban bincike da tsiwurwurin ci gaba. A halin yanzu ta na jagorancin wani tsiwurwurin binciken aikin gona mai suna (Kyautatawan jindadin iyali ta hanyar yin gona mai shuke – shuke iri

Babban ayyuka da subuwar al’adu

Page 7: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

7

dabam dabam cikin gonakin matan kasan Niger). Wata gidawniya mai suna Mcknight Foundation ta dauki nauyin wannan bincike mai ba mata izni su nuna mafi muhimman bukatun su da manufofin binciken saboda masanan kimiyya su taimaka mu su wurin aiwatarwa da bincikawa. Wanta Malama mai zurfin ilimi Doctor Bettina Haussman wanda ta ke mai bincike sa’annan malamar jami’a Hohenhein kuma itce masaniya kimiyya mai sadarwa don wani kungiya mai taimakawa wurin binciken shuke – shuke cikin Afrika ta yamma mai suna Mcknight Foundation Collaborative Crop Research Program ta goyi bayan wannan hidima mai sakewan matsayin manoma na gargajiya don a karfafa matsayinsu na zamani sosai dangane da zancen bincike.

Rediyo Binta

FUMA Gaskiya ta kafa wata tashar rediyo na karkara a cikin garin serkin hausa da manufan sanarwa manoma da ci gaban garin. Tashar

rediyo nan na yada labarai iri dabam dabam da ya shafe dangantaka da ke tsakanin shuke – shuke da dabbobi da halin zamani jama’a har da kwayoyi na gida dabam dabam da kasancewa an dace, da jigajanci yanayi, da yin regakafi domin kwari da farashin babban abinci, da yin amfani da taki da dabarun noma. An kafa tashan rediyo ne bayan wata mata mai suna Binta ta bukace haka. ko da yake ta rasu cikin shekara dubu biyu da bakwai ne (2007), an dibiya sunan ta kan tashar ne don a girmama ta. Tashar na watsar da labarai masu kyau da ilmantawa manoma, musamman mata soboda yawancin iyalai na amfani da rediyo. Da wuya ne manoma mata da ke da Zama cikin yankunan karkara su samu labarai su da kansu, saboda haka su na dogara sosai kan mazajensu, danginsu da makwabta su don samun labarai. Ta wani kashi, tashar na bakinta al’amarin rashin daidaito tsakanin maza da mata game da samun labarai aikin gona. Rediyo Binta na barin Rediyo Gabi, wanda kuma yake tashar mai aiki cikin yankunan karkaran jahar Maradi ta ci amfanin takardar shirin ta.

“Wannan sauyan ra’ayi mai ban sha’wa na matsayin ainihin sabuwar al’ada da wani irin babban ci gaba ne (saboda sokewan al’ada gargajiya zuwa ga al’adan zamani) a cikin ci

gaban aikin noma. Cikin dabi’a na asali dai, masanan kimiyya ke kawo ra’ayin tsiwurwuri sai kuma su yanke shawara akan yadda za a tafiyar da bincikin: abinda da masanan kimiyya ke

daure wa gindi. Da abinda na sani wancan harka bai da mai Kamar sa cikin Afrika ta yamma.”Doctor Bettina Haussman

Page 8: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

88

Tasiri

TASIRIN AIKIN GONAMayar da hankali da FUMA Gaskiya ta yi akan Karin wannan noma da ke kula da dagantakan da ke tsakanin shuke – shuke da dabbobi da tasirin wancan dangantaka akan amfani gona, da takin rubebbun dabobi da shuke – shuke da sassautawa ko kashen kwari ba tare da sunadarai ba (Nan, a na sa kwari su cinye kwari ne don a hana barnansu) na kyautatawa amfanin da kasan gona ke samu saboda dangantakan da ke tsakanin ta da dabbobi da shuke – shuke; Wannan na kuma kyautata kewayen sinadarin gina shuke – shuke.

A shuka kwayoyi masu kama da wake da gujiya da sauran, tsakanin kwayoyi masu iri dabam dabam na kara ma kasa wani sinadari da ya ke bukatar shi kwarai mai suna nitrogen, sa’annan kuma ya na taimakawa wurin ragewa barnan muguwar ciyawa. Daukakawan aikin gonan babban abincinsu iri dabam dabam na karfafawan amfanin da shuke – shuke ke samu daga dabbobi da wasu shuke – shuke, (watau a na ce ma wannan cin amfani in situ agricultural diversity). Sa’annan ya na kare manoma daga talaucin nan gaba (Tunda ya sani cewa bai da rashin nasara ko da halin wuri ya zo da damuwa). Yin gonan irin shuke – shuke da su ka bambanta kwarai ta hanyar yin amfani da wadansu iri dabam dabam, misali mai suna yakuwa da ridi da tafasa (Cassia tora), a turance da kankana ko guna da tumatur da wadansu shuke – shuke na jawo hankalin kwari masu amfani (saboda su za su canye kwarin da ke da damuwa) sa’annan ya na kuma ba da manoman Karin armashi ko da zai fuskance wani damuwa daga tattalin arziki da yanayi. Shiri, na Karin kyaun amfinin gona da ake tafiyad da shi har yau ta hanyan binciken hadin kai cikin gona na ba manoma kwayoyin gida da suka daidaita da damuwan sauyin yanayi.

TASIRIN YAWACIN SHIRI AKAN ZAMAN JAMA’A DA TATTALIN ARZIKIYawan manoma da ke yin kwayoyi cikin FUMA Gaskia ya karu daga takwas zuwa abinda ya fi dari biyu tsakanin shekara dubu biyu da taskwas (2008) da shekara dubu biyu da goma sha biyu (2012).

Wancan bazuwa ya bude ma yan kungiyan kofofi da dama samun aiki, kuma ya tabbatar cewa yan kungiya sun samu kwayoyi masu daraja kwarai. FUMA Gaskiya ta kimanta cewa ta saukaka samun amfanin gona da irin gero amintacce da ingantaccen kwaya cikin shakara biyar da suka gabatar; wannan ya haifad da kudi mai kimani a dollar Amerika dubu talatin da shida (US$36,000) kudaden da aka samu sun shiga cikin asusu mai kewayewa don karfafawan Karin jarinta cikin noman iri da karfafawar lafiyar jama’a da hidiman ilimi, kamar yadda ake bukatan a taimaka ma manoma cikin lokacin jin wuya, misali lokacin fari ko lokacin kaka da kudin amfanin gona ya sauka. Wannan shirin noman iri na kara ma manoma hanyar samun wannan shuka mai sunna cultivar a turance. (Nan, a na hada shuke – shuke biyu don a samu guda da zai fi amfani) da ke hana tsoron rashin abincin. Inagantacce wannan cultivar na geron lu’ulu’u ya yalwata amfani gona fiye da na da sau biyu (100%). Wadannan skuke – shuke (cultivar) masu saukin girma na balaga da sauri kuma na kawo abinci cikin farkon watannin damana lokacin da mafiyan amfanin gona bai nuna ba. Kuma tallan geron lu’ulu’u mai sunadarai gina jiki a turance iron da zinc ya taimaka wurin ragewar kwamason mata da yara.

FANNIN UNSAYawan matan kungiyar FUMA Gaskiya ya kasance hamsin da biyu ne daga cikin dari cikin adadin yan kungiyan, sa’annan wani adadin shirye-shiryen kungiyan ya sa ido musamman cikin al’amuran mata ne don su kasance masu cin amfani. Da kyar mata su samu kasa don noma cikin kasan Niger, kuma ko da sun samu sai ya kasance bai da girma, sa’annan bai da albarka. FUMA Gaskiya ta soma wani dabara na yin aikin lambu don ya karfafa mata su yi aikin lambu kusa da gidajen su lokacin fari soboda ya warware wancan damuwa. A na ilmanta da mata don su yi amfani da kayan gargajia (na gida) da ba wuyan samun su, misali tokan itace da tsarkakken bauli ko fitsari don Karin sakamako da albarkan kasa. Wadannan gonaki (lambu) na kawo ma iyalai abinci iri dabam dabam; ya na kuma kara kyaun

Page 9: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

9

abinci kamar yadda ya ke ba mata wani yanci game da yi ma iyali abinci.

Mata suna kunshe a cikin jarrabawar shuke — shuke iri dabam dabam, kuma mata na kimantawa halayen shuka da su ka fi so dabam da na mazan. An amince da ra’ayoyin su, da abinda su ka fi so kuma an yi jawabin wannan game da zaban kubewa iri dabam dabam, da yakuwa. Mata kuma ke da alhakin ganowan albarkataccen gero, mai yi shuke – shuke da ya ke mafi daraja game da shuka mai zuwa. Wadannan iri dabam dabam na nuna cewa nan gaba, ya isa kwarai yin amfani da shi a cikin wadansu yankunan sahel kuma ya iya taimaka kan zancen halin samu isasshen abinci cikin jahar. Wannan babban jawabin manoman karkara game da sabon gero ya sa mata sun zama sanannu mutane, kuma darajan su ta daukaka.

Wani tsiwurwurin FUMA Gaskiya na kwanaci da Mcknight Foundation ya dauki nauyin shi zai mayar da hankali musamman akan manoma mata da zancen jinsi da ya shafe yin gona cikin kasar Niger da batun abincin iyali. Wadannan manufofi sun nuna alkawarin FUMA Gaskiya dangane da daukakawar ilimin manoma mata, da karfafawar su.

TASIRIN SIYASAR FUMA GASKIYAWannan dangantaka da ke tsakanin kungiya mai suna International Crops Reseach Institute for Semi arid Tropics (ICRISAT) - watau cibiya

mai binciken shukan gona a cikin kasashe da kusan sun bushe, ba ruwa da Institut National de Recherche Agronome du Niger watau cibiyar kasa da ke da alhakin binciken shuka da FUMA Gaskiya ya kawo masa babban martaba da lambar girma na kwarai mai suna ICRISAT Partnership Award cikin shekara dubu biyu da goma (2010). Wancan tarayya na hadin guiwar ya ba kungiyoyi masu ba da gudummawa, da yin bincike, da yin siyasa sun amince da kimani hadawan. Kungiyoyin manoma cikin binciken gona da daukan manufofi, kungiyan ICRISAT ta ambato, cikin rahoto ta na shekara (2010) cewa hadin gwiwar da FUMA Gaskiya ya kasance abin kwatance da mai kara kuzari ne dangane da ci gaban manufofin ta game da bincike cikin sahel. ICRISAT ta yi karin shaida cewa FUMA Gaskiya abokin tarayya ne da ‘’ya fita dabam’’ a cikin shekaradububiyu da goma (2010).

FUMA Gasikiya ta sa hannu cikin bincike mai suna’Gestion integree Dela Mineuse De I’Epi du Mil’. (GIMEM) a Hausa Hadin kai a tare don kokawa da zuzuda, wanda kungiyar Mcknight Foundation Collaborative Crop Research Progam (CCRP) ya dauki nauyin hidimar. Bincike na da ainihi jarrabawa kan kula da hanyoyin hanawar barna wannan tsutsa mai hallakar amfafin gero. Sunan kwaro ne ‘zuzuda. Gwamnatin kasan Niger ya daukaka Dr. Ibrahim Baoua wanda ke aiki a ma aikatar bincike ‘INRAN’ CERRA saboda kokari da ya yi game da yaki da ya yi domin ya fid da wannan muguwar kwaro mai suna ‘zuzuda. Wannan fitarwa da ya samu ya jawo hankalin gwamnatin zuga ga karin goyin baya game da binciken aikin gona da shigar kungiyoyin manoma wurin kai bishara.

Page 10: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

10

DANWAMMAKudade da a ke Tarawa daga yankungiyan kerike da FUMA Gaskiya, saboda haka suna da isar wurin tattalin arziki. kurgiyan an Kafata a tafarkin demokradiya (kowa na da hannu cikinta) da nuna gaskiya ne kuma yan kungiya da kansu ke mulkin ta saboda haka ta na kawo musu babban jin dadi cewa kungiya na su ne kuma su ke mulkin ta ba tare da wani ba. FUMA Gaskiya ta aiwatar wani tsari inda manoma da kansu sun shiga kwarai cikin noma da sayar da irin zamani. wanan shiri na karuwa ne ko wani shekara; abin nuna cewa kungiya ta dawamma da dadewa. Girman yan kungiyar FUMA Gaskia (Wadansu kungiyoyi manoma na niyya su shiga cikin kungiyar ko wani shekara) ya nuna cewa kungiyar ingantacce da dawamamme ne. Duk da cewa cikin irin wannan yankuni, samun yawan taimakon manoma na da wuya, FUMA Gaskiya na yin nata rabon aikinta na kungiya mai zaman kanta ta hanyar ba da manoma subuwar ilmi da ya shafe muhalli da dabbobi, da shuke — shuke, da sauran, da ilmin fasaha na zamani. Babban dangantaka da cibiyoyin bincike na sa FUMA Gaskiya ta samu taimakon cibiyoyi masu bayar da gudummawa don aiwatarwa tsiwurwurin hadin gwiwar cikin bincike da ke amfanar da manoma masu kananan gonaki.

MAIMATAWAHadin gwiwar FUMA Gaskiya da cibiyoyi binciken gona na saukaka musayan ilmin gwaninta na gona da ilmi zuwa ga manoma da adadin su ya wuce dubu goma sha biyu cikin Niger. Samun nasara dangane da jarrabawan darajar kwayoyi da aka aiwatar cikin serkin Hausa ya kawo karba da jarrabawan samfurin cikin wadansu kungiyoyin FUMA Gaskiya, har da sae saboua, El-kolta, Tessaoua, Dargue da Maiki. Ta marhalan jahar, yan kungiyan FUMA Gaskiya sun taimaka zuwa ga musayar ziyara tare da kungiyoyi manoma da ba su fito Niger ba, misali ‘Union des Agriculteurs du cercle de Tominian cikin Mali, da Union Departemental des producteurs de Nobere’ (kungiyar manoman Tominian cikin Burkin Faso) da kungiyar kamwinson

group daga Ghana. wancan tsarin neman ilmi na manoma masu matasyi guda wajen aikin gona na saukakawan musayan ilmi da ya shafe sabuwar fasahan gona da shuke – shuke. Ya na sa manoma su maimata mafi ra’yoyi masu kyau da sabuwar fasahan noma da shuke — shuke da ya fito daga cibiyoyi da ke cikin jahar. Musanya manoma kuma na karfafawan sabuwar ilmi, misali, kwankwanton gonan ‘fonio’ da su kansu ke yi akan matsayin sa na abincin dabbobi. (A wani wuri dabam cikin Mali dai babban abincinsu ne).

ABOKANIN TARAYYAHadin gwiwar da cibiyoyin bincike musamman cibiyan binciken shuke — shuke na kasashen duniya na yammacin sahara (ICRISAT), sa’annan Institut National de Recherche Agronomigue du Niger. (Cibiyan bincike shuke – shuke na kasan Niger) da jami’a ‘Hohenheim’

Dawamma da maimatawa

Page 11: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

1111

ya ba yan kungiyan FUMA Gaskiya daman sa hannu cikin ayyukan binciken shuke – shuke. Wadansu hadin gwiwar da ke tsakanin manoma da masu bincike misali Wadanda Mckinght Foundation ya dauki nauyin su, sun kawo matukar ci gaban tsarin kwayoyi na gida kuma ya ba da yawan amfanin shuke – shuken babban abinci da manoma suka zabi, sa’annan ya kawo sabuwar dabarun mulkin kwari. A halin yanzu Mcknight da iyalin sa sun dauki nauyin wani tsiwurwuri mai manufan manoma mata cikin jahar maradi don ya kyautata abincin iyalai da samun jinginan abinci mai gina jiki. Ma’aikatar gwamnatin Jamus mai gama kai wajen tattalin arziki da ci gaba ya dauki nauyin tsiwurwuri biyu da ya shafe FUMA Gaskiya;

guda na da manufan shuke – shuke iri dabam dabam da ke karbuwan canzan yanayi (tsiwurwurin CODE-WA) sa annan guda kuma na bincikan damuwan da ke cikin fasahar yin gona da ya shafe shuka da dabbobi da sauran halitta da ke cikin kasa damuwansa tare da noman Sahel. Cibiya mai suna The Bill and Melinda Gates Foundation ya tallafa aikin bincike da ke da manufan hadawan fasahan yadda ake tafiyar da zukiyar halitta da sakewan tsarin shuke - shuke don yin gero, da kara kyaun geron lu’ulu’u’. Kungiyar abinci da noma da ke karkashen Majalisar Dinkin Duniya ta taimaka ma FUMA Gaskiya don sayawa da rabawan kwaya mai yawa da taki domin amfanin kungiyoyin manomansu.

“Muna kuma gudanar da al’amuran hadin gwiwar masu kamar da na farko da kungiyoyi dabam dabam ko’ ina cikin jihan – Misalai masu muhimmanci na ilmin kimmiya mai tare da

fuskan dan Adam’ – Ilmin kimmiya da ke da tasirin tsaye akan mazaunan karkara alhalin ya na sarrafawa kayan jama’a na duniya.’’

ICRISAT

Page 12: FÉDÉRATION DES UNIONS PRODUCTEURS DE MARADI · PDF filede producteurs de Maradi Gaskiya, Niger. Manufar binciken Equator masu bi juna, watau Equator Initiative Case Study Series,

KARIN DUBE-DUBE ■ FUMA Gaskiya Flicker page

■ ICRISAT annual report 2010

■ Christinck A., Diarra M. & Horneber G. 2014. Innovations in seed systems: lessons from the CCRP-funded project “Sustaining farmer-managed seed initiatives in Mali, Niger, and Burkina Faso.”

■ CODE-WA project description

■ U.S. Geological Survey. 2012. A climate change analysis of Niger

Equator InitiativeSustainable Development ClusterUnited Nations Development Programme (UNDP)304 East 45th Street, 6th Floor New York, NY 10017Tel: +1 646 781-4023 www.equatorinitiative.org

UNDP (Kungiyan Majalisan Dinkin Duniya mai kula da al’amarin ci gabansa) na hadin gwiwar da mutane na kowane marhalan zaman tare domin ta gina kasashe da za su iya jure wa kowane tarzoma mai matukar; sa’annan kuma zasu kasance su ne dalilin dawamammen Karin girma wanda zai kyautata ma kowa rayuwan kwarai. Ta kasa a cikin kasashe dari da sabain dai, muna taya wa kowa tsammani game da zaman duniya tare da tsinkaya na gida don mu taimaka wa mutane wurin samun karfi da iko da ginan kasashe masu armarshi.

Wannan manufar na Equator na hadawan Majilisan Dinkin Duniya da gwamnantoti, da mazaunan kasashe, da yan sana’a, da kungiyoyin gida masu harka, da mutane da al’amarin ya shafe su domin ganewa da daukakawan mafitan dawamammen ci gaba na gida don mutane, da hallita da al’ummomi masu armashi.

Rubuce Rubucen “Equator a cikin shekara dubu biyu da goma sha biyar” ©2015Ko wane bai da hakki ya buga ko ya kwaikwayo wannan littafi sai da sanin marubta

ABOKANIN TARAYYAN TSIWURWURIN

ABOKANIN TARAYYAN MANUFAR IKWAITA

Empowered lives. Resilient nations.

Empowered lives. Resilient nations.